Ruwan saman da aka yi kamar da bakin kwarya ranar Talata a karamar hukumar Jama’are da ke jihar Bauchi ya barnata gonaki akalla 1,567.
Ruwan sama, wanda aka dauki sa’o’i sama da 20 ana yi, ya shanye gonaki da amfanin gona a ƙauyuka bakwai dake karamar hukumar Jama’are.
Shugaban karamar hukumar Samaila Jarma ya tabbatar da haka wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ranar Alhamis a Jama’are.
Jarma ya ce ambaliyar ya shafi kauyukan Jogiyal, Yola, Doko-Doko, Gongo, Kabigel, Digiza da Massalachin Idi yankin garin Jama’are, a sakamakon kwararowar ruwa daga rafin Jos sakamakon ruwan saman da aka yi na awwi masu tsawo a ranar Talata.
“Mun tsinci gawarwaki biyar malemale a gefen teku bayan ambaliyar ya janye.
“Mun kuma gano cewa daya daga cikin mutum biyar din da suka mutu mazaunin daya daga cikin kauyukan da ambaliyar ruwan ya auku ne.
“An binne gawarwakin bisa ga ka’idojin da suka dace bayan an gudanar da cikakken bincike domin tantance asalin su.
“A yanzu haka mun dauki hotunan su domin ci gaba da bincike.
Jarma ya ce majalisar ta kuma kaddamar da wani kwamiti domin tantance barnar da ambaliyar ruwan ya yi domin mika rahoton ga gwamnatin jihar saboda ta daukar matakin da ya dace.
Ya ce zuwa yanzu majalisar ta raba kayan abinci da sauran kayayyaki ga wadanda ambaliyar ya shafa don rage radadin wahalar su.