Ambaliyar gurɓataccen takin zamani ta mamaye kasuwanni -Hukumar SON

0

Hukumar Kula da Ingancin Kayayyaki ta Najeriya (SON), ta nuna matuƙar damuwa dangane da abin da ta kira ambaliyar gurɓataccen takin zamani a kasuwannin Najeriya.

Hukumar ta ja kunnen masu sassafa takin zamani su da manya da ƙananan dillalan takin zamani su riƙa bin ƙa’idojin da hukumar ta gindaya wajen cika sharuɗɗan samar da ingantaccen takin zamani.

Ya ce su riƙa tabbatar su na sayar da takin zamani nagari ba gurɓatacce ba ga manoma.

Kodinetan SON na Jihar Kano, Yunusa Muhammad ne ya yi wannan gargaɗi da jan-hankali a ranar Alhamis, lokacin da ya ke ganawa da masu ruwa da tsaki a harkokin sarrafawa da sayar da takin zamani a Jihar Kano.

Muhammad ya ce taron ganawar da su ya zama wajibi, ganin yadda ake ƙara samun yawaitar gurɓataccen takin zamani a kasuwanni.

Ya ce Hukumar SON za ta tabbatar cewa manoma ba su sayi takin zamani mai algushu ba.

Ya ƙara da cewa nagartaccen takin zamani shi ne ƙashin bayan samar wadatar amfanin gona mai yalwa. Kuma takin zamani ya na bunƙasa harkokin noma sosai.

Ya ce idan SON ta samu haɗin kan masu sarrafa takin zamani da manyan dilalan sa, to hukumar za ta magance matsalar gurɓataccen takin zamani da ake yawan kukan ana ambaliyar sa a kasuwanni.

A ƙarshe Muhammad ya bai wa masu sarrafa takin zamani kwanaki 45 su bankaɗo ɓatagari a cikin su.

Share.

game da Author