Allah yayi wa matar tsohon dan gwagwarmayar siyasa Danjani Hadejia rasuwa

0

Hajiya Ummah daya daga cikin matar marigayi Danjani Hadejia ta rasu ne a asibitin Babban Birnin tarayya dake a Abuja.

Danjani Hadejia wanda abokin gwargwarmayar siyaya ne na Malam Aminu Kano shi ya rasu a watan 11, 1991 a Birnin Kano.

Hajiya Ummah ta rasu ne yau Lahadi 8 ga watan August, 2021 a Abuja, bayan shafe lokaci mai tsawo tana fama da jinya.

Ta rasu shekara talatin bayan rasuwar mijinta Muhammadu Danjani Hadejia.

Ta rasu ta bar ‘ya’ya bakwai da jikoki da dama, cikin ‘ya’yanta harda da Jamilu Muhammad Danjani Babban Jami’in Dan Sanda dake aiki a sashen bincike dake a Abuja.

Za’ayi jana’izarta gobe lilitin da safe misalin karfe takwas a layin Kabobo dake unguwar Fagge a cikin kwaryar Birnin Kano, Allah ya gafarta Mata ya kamu kyautata bayanta.

Share.

game da Author