Tsohon Ministan Sufuri Femi Fani-Kayode ya maida kakkausan raddi ga waɗanda su ka riƙa suka da zagin sa a soshiyal midiya, don ya halarci ɗaurin auren Yusuf Buhari a Bichi.
Inda Femi ya fi shan caccaka shi ne tun a ranar Alhamis, jajibirin ɗaurin aure, inda ya watsa hoton sa a Kano, tare da Ministan Sadarwa, Isa Pantami.
A hoton dai Femi Fani-Kayode Kayode ya kira Pantami “aboki kuma ɗan’uwa.”
Lamarin ya janyo masa caccaka sosai a soshiyal midiya kafin da kuma bayan halartar ɗaurin auren da ya yi a Bichi.
Sai dai kuma a ranar Lahadi, Femi Fani-Kayode ya sake fitowa a soshiyal midiya ya yi wa masu sukar sa tatas.
An riƙa sukar sa ne ganin yadda a baya ya riƙa kiran Pantami da sunaye da laƙabin, “mai kisa da sunan addini”, “ɗan ta’addar da bai tuba ba”, “mai sha’awar zubar da jinin bayin Allah.”
Hoton da aka nuno Kayode da Pantami na gaisawa ya ja hankalin jama’a sosai.
Raddin Femi Fani-Kayode:
“Duk mai jin haushin na gaisa ko ko na kira Minista Pantami aboki kuma ɗan’uwa, to ina ruwan sa. Idan har yanzu ba ji daɗin abin da na yi ba. Allah ya sa baƙin ciki ya kashe ka.
“Ni addini na ya koya min yafiya ga duk wanda ya tuba ya gane abin da ya yi ba baya kuskure ne. Kuma na gane ba tubar-muzuru ya yi ba.
“Sannan addini na ya koya min idan aka miƙo min hannu mu gaisa, to ni ma na miƙa masa hannu mu yi masabaha.
“Shin wai ma ina ruwan ku da zaɓar min wanda zan yi gaba ko abokantaka da su?
“Duk mai kumfar baki har yanzu don na halarci bikin ɗan Shugaba Buhari, Allah ya sa ya yi bindiga ya fashe ya mutu don baƙin ciki.
“Ku je ku ci gaba da faffakar banza da wofi, kamar zakaran da aka gutsiri wa kai. Ko ya yi faffaka ya na tsalle-tsalle, a banza, tunda dai mutuwa zai yi.”
Femi Fani-Kayode, ya ci gaba da antaya wa masu sukar sa baƙaƙen kalamai.
“In banda rashin kunya, ba ku ga laifin Buba Galadima ba da ya halarci ɗaurin auren, sai Ni? Ga Atiku Abubakar ya je, ga tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan duk sun halarta. Su duk ba su yi laifi ba sai ni.”
Femi Fani-Kayode ya ce don ya halarci taron ɗaurin aure, hakan bai canja masa siyasar sa ko alƙiblar sa ba.
Discussion about this post