Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shekaru 10 da aka shafe riƙe da Ƙudirin Dokar Fetur (PIB) a Majalisa ya janyo wa Najeriya asarar dala biliyan 50 da ya kamata masu zuba jari su zuba a harkar mai domin bunƙasa fannin.
Buhari ya yi wannan jawabi a wurin ƙwarya-ƙwaryan bikin sa wa Ƙudirin Dokar Fetur (PIB) hannu, inda a yau ta zama Dokar Bunƙasa Harkokin Fetur ta 2021 (PIA 2021).
Daga nan Buhari ya yi kira ga al’ummar yankin Neja-Delta da ake haƙo fetur da su ka raina kaso 3% bisa 100% na rarar ribar man da su yi nazarin ƙudirin dokar filla- filla, domin su ga alfanun da ke cikin sa.
“Rashin kishin ƙasa da aka nuna a gwamnatocin baya ya haifar da rashin bunƙasar harkokin man fetur da gas a ƙasar nan.” Inji Buhari.
Sannan kuma ya ce wannan doka za ta bada dama masu zuba jari su garzayo su antaya maƙudan kuɗaɗe a harkar fetur da gas, ta yadda za a bunƙasa harkar, a samu aikin yi, tattalin arziki ya bunƙasa, kuma a daina balbala asarar iskar gas a ƙasar nan.
Ya ƙara da cewa hannun da ya sa wa ƙudirin ya zama doka ya zama an kawo ƙarshen shekaru goma a aka shafe ana zaman zullumin rashin tabbas a harkar bunƙasa fetur da gas.
PREMIUM TIMES ts buga labarin da Ƙaramin Ministan Fetur, Timipre Sylva ya bayyana cewa Buhari zai yi jawabi, kuma shi Minsitan ya nuna cewa bai ga dalilin ƙoƙarin raina kashi 3% bisa 100% da ‘yan yankin Neja-Delta ke yi ba.
Sylva ya jaddada cewa yankunan da ake haƙo fetur ba su cancanci kason fiye da 3% ba.
Ƙaramin Ministan Fetur, Timipre Sylva ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa Dokar Inganta Fannin Man Fetur ce don a gaggauta samun masu zuba jari.
Da ya ke amsa tambayoyi a Abuja a ranar Talata, Sylva ya ce a ranar Alhamis Shugaba Buhari zai yi bayani dalla-dalla yadda wannan doka ta ke da kuma duk abin da ya shige wa mutane duhu dangane da batun Rabon Arzikin Mai da ke ƙunshe a cikin dokar.
Da ya ke magana dangane da al’ummar yankin Neja-Delta, waɗanda su ka raina kashi 3% bisa 100% na rarar ribar fetur ɗin da ake haƙowa a yankin su, Sylva ya ce shi bai ga abin tayar da jijiyar wuya kan lamarin ba.
“Ai har gara ka karɓi kashi 3% bisa 100% wadda ka ke da tabbas cewa lallai akwai su, maimakon jiran kashi 100% bisa 100% da ba ka tabbas a kan su.
“Ni ɗan yankin Neja-Delta ne. An sa dokar nan don a jawo hankalin masu zuba jarin ƙara haƙo mai a yankin. Yin haka kuma ai yankin zai bunƙasa sosai kenan. Domin idan ba a zo an haƙo mai a yankin ba, shi kan sa yankin ba zai samu komai ba.
“Shekaru 10 da su ka gabata, Najeriya na da ɗanyen mai ganga biliyan 37 kwance a ƙasa. Amma maimakon a samu ƙarin haƙo mai, sai ma ƙasa ya yi da miliyan uku. Sai fa kwanan nan da aka fara tashi tsaye.”
Da Sauran Rina A Kaba:
Sylva ya ce daga yanzu fetur ne da kan sa zai riƙa yanka wa kan sa farashi a hannun ‘yan kasuwa. Wato kasuwa ita ce alƙali.
A kan haka ne ya ce ba za a yi saurin fara amfani da dokar PIB ba tukunna, har sai an yi nazarin yadda za ta shafi talaka da kuma hanyoyin magance abin da zai iya faruwa.
Sannan kuma ya ce gwamnati za ta zauna da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago domin a tarbi duk wani abin da ka iya zuwa nan gaba.
Wannan kalami dai na nufin akwai yiwuwar idan aka fara amfani da Dokar ‘PIB’, farashin litar fetur za ta tashi sama sosai.
Dama an daɗe ana raɗe-raɗin cewa litar mai za ta koma naira 350.
Discussion about this post