AFGHANISTAN: Sharuɗɗa 9 da sabuwar gwamnatin ‘yan Taliban ta gindaya a ƙasar

0

Ƙungiyar Taliban da ta sake ƙwace ragamar mulkin Afghanistan a ranar Lahadi, ta kafa sharuɗɗan da ta ce za a tafi a kan su a rayuwa da zamantakewar ƙasar a ƙarƙashin ikon ta.

Cikin tattaunawa da manema labarai a karon farko da Taliban ta yi a ranar Talata a Kabul babban birnin jihar, Kakakin Yaɗa Labaran Taliban, Zabihullah Mujahid, ya bayyana cewa:

1. Za a kare mutunci, ‘yanci da haƙƙin mata a Afghanistan, a bisa tsarin Musulunci.

2. Za a bar mata su fita su yi aiki a bisa tsarin Musulunci.

3. Za a bar mata su riƙa shiga cikin jama’a, su na harkokin su bisa tsarin Musulunci.

4. Gwamnatin Taliban na buƙatar dangantaka ta lumana tsakanin ta da ƙasashen waje.

5. Gwamnatin Taliban ba ta buƙatar abokan gaba na cikin gida ko daga wajen ƙasar.

6. Mu na kira ga waɗanda su ka tsere su ka yi dafifi a filin jirgi cewa kowa ya koma gida, ya yi zaman sa lafiya.

7. Kafofin yaɗa labarai na da ‘yancin su. Amma kada su wuce gona da iri su shiga ɓatanci ga tsarin al’ummar ƙasar mu.

8. An yafe wa kowa babu wani da za a bi da bi-ta-da-ƙulli.

9. Mata su fito su shiga gwamnati, su yi aiki a bisa tsarin da Musulunci ya gindaya.

Share.

game da Author