AFGHANISTAN: Na Janye Sojojin Amurka Saboda Sojojin Ƙasar ba su kishin murƙushe ‘Yan Taliban – Joe Biden

0

Ga dalilan Amurka na janye sojojin ta daga Afghanistan, bayan sun shafe shekaru 21 su na yaƙi a ƙasar da Amurka ta fi daɗewa ta na ya yaƙi, kuma ta fi kashe kuɗaɗe.

1. “Amurka ta shafe shekaru 21 sojojin ta na yaƙi a Afghanistan.

2. “Tun wancan lokacin dama Amurka ta ba girke sojoji ta Afghanistan da nufin su yi zaman dirshan ko taya gwamnatin ƙasar riƙe mulki ba.”

3. “An tura sojoji ne domin daƙile ƙungiyar Alqa’ida waɗanda su ka riƙa kai wa Amurka hari a cikin gida.

4. “Saboda Sojojin Amurka sun je Afghanistan ne kawai don hana a sake kai wa Amurka irin mummunan harin da aka kai mata a lokutan harin ‘September 11’ ko makamancin sa.

5. “Amurka ta samu nasarar daƙile ta’addancin ‘yan Alqa’ida, an murqushe ƙungiyar kuma an kashe shugabannin da su ka assasa ta.

6. “Amurka ta taimaka an kafa gwamnatin da ta bai wa kowa ‘yancin walwala da samar da zaman lafiya bakin gwargwado, bayan murƙushe gwamnatin Taliban mai goya wa ‘yan ta’adda baya.

6. “Amurka ta kashe fiye da dala tiriliyan 1 wajen horas da sojojin Afghanistan da sauran jami’an tsaro da kuma samar masu da makamai. Da kuma ɗaukar ɗawainiyar sojojin Amurka da wasu hidindimun gwamnatin ƙasar.

8. “An girke Sojojin Amurka 300,000 a Afghanistan, masu yawan da akasarin ƙasashen Taron dangi ba su ma da yawan sojojin.

9. “Duk da wannan ƙoƙarin da mu ke yi, sai muka fahimci su sojojin Afghanistan ba su ma da zuciya ko ƙoƙari da kishin tsare ƙasar su daga ‘yan Taliban masu ƙoƙarin sake ƙwace mulkin ƙasar.

10. Don haka Amurka ba za ta yi wa Afghanistan yaƙin da sojojin ta ba su da kishin yi wa ƙasar ta su yaƙi ba.

11. “Amurka ta shafe kusan shekaru 21 a Afghanistan ta na yakin da ta fi kowane daɗewa tsawon shekaru, kuma ta fi kashe maƙudan kuɗaɗe a kan sa. Musamman ganin yadda waɗanda ake yaƙin don su, ba su da cikakken kishin hana Taliban ɗin sake ƙwace ƙasar.

12. “Lokacin da Shugaba Ashraf Ghani ya zo nan Amurka, na shaida masa cewa Amurka za ta janye sojojin ta. Ya zama tilas Afghanistan ta tashi tsaye ta kare kan ta da kan ta, domin Amurka ta yi dukkan ƙoƙarin da ya wajaba ta yi wa ƙasar.

13. “Kuma na faɗa wa Ghani cewa tilas gwamnatin sa ta tashi tsaye ta daƙile mummunar satar kuɗaɗen da jami’an gwamnatin sa ke yi.

14. “Ghani ya ce min duk za a yi hakan, amma har ya gudu ya bar ƙasar babu wani canji da aka gani.

15. Ya zama tilas Amurka ta kwashe sojojin ta, domin waɗanda ake tayawa yaƙin ba su da kishin kare ƙasar su. Shugaban Afghanistan ɗin kan sa tserewa wata ƙasa ya yi.

16. “Yaƙin nan ya janyo wa Amurka asarar sojoji da dama da asarar sauran rayukan jama’a. An bar mu da gawarwaki kwance hululu cikin maƙabartu birjik.

17. “Saboda haka ni dai ba zan ci gaba da maimata kuskuren da muka riƙa yi a baya ba.

18. “A lokacin da ina mataimakin Shugaban Ƙasa, ni kai na yi iyakar bakin ƙoƙari na. Na je Afghanistan sau huɗu. Duk manyan garuruwan su ba wanda ban taka ba. Har Khandahar na je duk ina ƙara wa sojojin su ƙwarin guiwa.

19. Ni ne Shugaban Ƙasa na 4 a zamanin Gwamnatoci 5 da su ka gaji wannan yaƙi.

20. Don haka a yanzu dai ne Shugaban Ƙasa. Alhakin komai a kai na ya ke.

21. Ba zan miƙa gadon ci gaba da zaman Sojojin Amurka a Afghanistan ga shugaban da zai hau mulki a baya na ba.

21. Amma za mu ci gaba da bayar da gudummawa, shawarwari, shiga tsakani da haɗa kai da ƙasashe da Majalisar Ɗinkin Duniya, domin samun mafitar Afghanistan.

22. A yanzu abin da za mu ci gaba da maida hankali a kai, shi ne kare Amurka daga duk wasu hare-haren ta’addanci ko daga waje, ko daga cikin gida.

23. “Mun tura sojiji 6,000 Afghanistan domin kwaso dukkan jami’an diflomasiyya na Amurka da sauran jama’ar ƙasar, sai kuma sauran ‘yan kasar da ta ke tare da mu.

24. Mun sanar da shugabannin Taliban cewa kada a kuskura a nemi hana Sojojin Amurka aikin kwaso jami’an mu baki ɗaya da sauran jama’ar da za su kwashe.

25. “A ƙarshe mun gargaɗe su cewa idan aka yi ƙoƙarin hana Sojojin Amurka yin aikin su, to Amurka za ta yi masu luguden wutar yi masu rugu-rugu.”

Share.

game da Author