ABUJA: Kotu ta daure wasu ‘yan mata biyu saboda yawon gulmace-gulmace a unguwa

0

A ranar Alhamis ne kotu a yankin Grade I da ke Karu, Abuja ta yanke wa wasu mata biyu hukuncin daurin watanni uku saboda yawan tada husuma da gulmace-gulmace a unguwa.

Alkalin kotun, Inuwa Maiwada, ya yanke wa Loveth Joseph mai shekaru 20 da Anita Francis mai shekara 19 wannan hukunci ne bayan sun amsa laifukan su tare da rokon sassauci daga wurin alkali.

Maiwada ya basu zabin biyan tarar Naira 10,000 kowannen su ko su yi zaman kurkuku na tsawon watanni uku.

Lauyan da ya shigar da karar Vincent Osuji ya shaida wa kotun cewa a ranar 30 ga Yuli ‘yan sanda da ke sintiri cikin dare da sifeto Aghole Stephen da ke aiki a ofishin‘ yan sanda na Karu suka kama wadannan mata suna tada husuma a unguwar su, gaba daya unguwa ya yamutse saboda tsigudidin, da yawon gulmace-gulmace da wadannan yan mata suka haddasa.

Osuji ya ce da ‘yan sanda ke binciken wadannan mata sun ƙasa bada dalilin fitowar su waje a cikin daren da aka kama su.

Ya ce laifin da wadannan mata suka yi ya saba wa tanadin sashe na 198 na dokar manyan laifuka.

Wadannan mata ba su zama wuri daya, basu nan basu can, su kulla bala’i a nan suje can su kulla.

Share.

game da Author