ABIN KAMAR A DIRAMA: Wata ‘yar fim ta sha alwashin zama shugabar Najeriya

0

Yayin da a Liberiya ɗan wasan ƙwallon ƙafa George Weah ya zama shugaban ƙasa, kuma shi ke kan mulki a yanzu haka, a Najeriya kuma wata ‘yar fim ta bayyana wa duniya cewa ƙudiri aniyar shugabancin ƙasar nan.

Tonto Dikeh, ‘yar fina-finan Nollywood, ta bayyana wannan buri na ta a shafin ta na Instagram a ranar Talata.

A shafin na ta na Instagram dai ta na da mabiya fiye da mutum miliyan 6.8.

Kwanan nan Tonto ta bayyana soyayyar da ta yi da wani attajirin matashin ɗan siyasa, mai suna Prince Kpokpogbi ɗan asalin Jihar Delta.

Tonto Dikeh wadda ‘yar asalin Jihar Ribas ce, ta kuma sanar cewa kuma ta bayyana hotunan na ta a shafin Instagram masu nuna cewa a wata babbar makaranta ce aka yi su.

Ta bi hotunan ta rubuta: “To ni dai na koma makaranta, saboda na ƙudiri aniyar zama shugaban Najeriya”

Ba ba ta dai bayyana bayyana sunan makarantar ba. Dama ko a cikin 2020 da mujallar Ovation ta yi hira da ita, ta ce ta na sha’awar zama sanata, kuma wataƙila ta fara daga matakin na sanata a 2023, domin share hanyar zama shugaban ƙasa.

Share.

game da Author