Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II da aka yi murnar zagayowar ranar haihuwarsa a ranar 31 ga watan yulin shekarar dubu biyu da ashirin da daya (31/07/2021), ya bayyana a cikin wata tattaunawau da jaridar Thisday tayi da shi. A inda Mai Martaba yace:
“Da farko dai ban goyi bayan yunkurin gwamnatin jihar mu na ciyo bashi har na dala biliyan daya da miliyan dari takwas ($1.8) ba, domin wai a gina layin dogo, duk da yawan yaran da basu zuwa makaranta a jihar, da kuma rashin samun abinci mai gina jiki ga yaran.”
“Na biyu, don samun zaman lafiya a jihar mu, nayi kira akan cewa don Allah a daure ayi zabe na gaskiya, kar ayi magudin zabe, kuma nace duk wanda yayi nasara a bashi, wanda yayi rashin nasara yayi hakuri. Sannan kuma mun yi kira a zabi mutane nagari, wadanda suke kishin al’ummah, kuma suke neman ci gabansu. A gani na wannan hakki ne da ya rataya a wuya na, a matsayina na Sarki. Ban yi tsammanin hakan zai zama abinda zai sa aji haushi na ba. Amma nasan cewa kaddarar da Allah ya dora wa Bawa ba zai taba tsallake ta ba. Idan ma ban yi abinda ya kamata a gare ni ba, na yin magana, da fadawa masu mulki gaskiya, hakan ba zai sa in kara minti daya akan kujerar mulki ba, matukar ba haka Allah yaso ba. Nayi imani cewa, in dai har lokaci yazo to dole in bar karagar mulki, a raye ko a mace.”
Wasikar ma da aka kawo man tana dauke da cewa, wai ana zargi na da “KIN YARDA DA ABINDA GWAMNATI KE SO.”
“A takaice dai na zabi in bar mulki da DARAJA ta, da MUTUNCI na, akan in zauna a KASKANCE, tare da yin makauniyar biyayya ga wasu mutane da na san tsarin su mara kyau ne, kawai don in zauna akan gadon mulki, amma a wulakance, babu daraja.”
“Da kaina na zabi in ajiye karagar mulki, kuma har gobe ina alfahari da zabi na, kuma har yau ina cikin farin ciki game da yin hakan. Sannan ga shi kuma Allah yana kara bamu daukaka da daraja a cikin al’ummah, Alhamdulillah.”
Da Mai Martaba yake bayar da amsa akan tambayar da aka yi masa ta cewa, me yasa yake kalubalantar Gwamnati? Khalifah ya bayar da amsa, yana mai cewa:
“Tun lokacin da na zama Sarki, na san abun da zan tarar na wahala, amma hakan bai sa ni na tsaya ba. Na kan ce, in dai har a matsayinka na Sarki, kayi shiru, alhali al’ummah suna bukatar maganarka, saboda wai tsoron shugabanni, to ba sunan ka Sarki ba, sunan ka Bawa mai sanye da kayan sarauta.”
“Yanzu a matsayina na Khalifah na Tijjaniyyah a Najeriya, akwai nauyi na sama da mutane miliyan hamsin (50) a kai na, kuma hakika, muna bukatar ya zama an hada kai, an fuskaci kalubalen dake gaban mu, kamar ilimi, tallafi na sana’o’i, ci gaba na zamani, da makamantansu.”
Jama’ah wannan kadan kenan daga cikin tattaunawar da jaridar Thisday tayi da Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II.
Har koda yaushe, ina mai yin addu’a da rokon Allah ya taimaki Sarki, Allah ya kara masa lafiya da karfin imani da nisan kwana da yawan shekaru masu yawa, masu albarka, masu amfani, amin.