Fitaccen dan wasan fina-finan Hausa, Adam Zango ya bayyana cewa a halin da yake ciki yanzu, a shirye yake ya hakura da farfajiyar fina-finan Hausa wato Kannywood, ya rungumi wata sana’ar.
Zango ya bayyana haka ne a hira da yayi da BBC Hausa a karshen makon jiya.
” Duk da zama fitaccen jarumi a farfajiyar Kannywood, burina shine a ce yau na daina wannan sana’a. Na rungumi wata sanar wacce ta fi wanda nake yi yanzu.
Zango ya ce idan har ya samu wata sana’ar da ta fi wacce yake yi yanzu, wacce ta fi kawo masa kudaden shiga, zai hakura da fim ya rungumeta.
” Babban burina shine ace na fice daga kannywood cikin kwanciyar hankali ba tare da na bar wa ‘ya’ya na abin fadi nan gaba ba. Shi ya sa fata na shine in samu wata sana’ar da tafi wannan in rungumeta salin-alin.
Zango ya taba fadin cewa ya ma fice daga Kannywood saboda bakincikin daukakar da Allah yayi masa a farfajiyar shirya fina-finan.
A wancan lokacin ya ce ya hakura da ita, ya komo Kaduna inda ya kafa ta sa farfajiyar ,ai suna Kaddywood. Sai dai bata yi tasiri ba inda daga baya ya koma Kannywood din ya ci gaba da harkar sa da sauran taurarai.
Bayan haka Zango ya bayyana wasu dalilai da ya sa ba ya kaunar ace wai zai hau jirgin sama kamar yadda abokan sa ke rige-rigen ace yau gasu a jirgin sama za su yi tafiya.
” Bana kaunar hawa jirgin sama ko kadan, hakan ya sa zai yi wuya ka ganni a jirgin sama wai zan yi tafiya. Tafiyar da nayi mai tsawo a rayuwa na ita ce Landan da na tafi. Itama duk awowin da aka yi a sama, idona kiru har aka isa birnin Landan.