2023: Osinbajo bai nuna sha’awar fitowa takarar shugaban ƙasa ba

0

Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ya nisanta Mataimakin Shugaba Yemi Osinbajo da wasu fastoci masu ɗauke da hotunan sa na neman shugabancin ƙasa a 2023.

Mataimakin na Buhari ya ce bai taɓa nuna sha’awar fitowa takarar shugaban ƙasa ba, kuma bai ayyana a sarari ko a ɓoye cewa zai fito takara ba.

Wannan bayani ya fito ne sakamakon yadda ake ta liƙa hoton Osinbajo a Abuja da Kano da kuma soshiyal midiya, ana nuna cewa shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na APC a zaɓen 2023.

Kakakin Yaɗa Labarai na Fadar Osinbajo, Laolu Akande ya shaida cikin wata sanarwar da ya sa wa hannu a ranar Laraba, ya nuna cewa Mataimakin Shugaba ya maida hankali ne wajen ayyukan gina ƙasa da ya fi sa a gaban sa. Don haka ba shi da lokacin bada umarni ko ɗaukar nauyin buga fastocin sa har ana liƙawa da rabaswa.

Daga nan sai ya yi kira ga masu yin wannan azarɓaɓin da su daina, domin shi dai bai nuna sha’awar fitowa takara ba kuma bai ce zai fito takara ba.

Tun bayan jigon APC da ake tallatawa, sai kuma Gwamna Yahaya Bello na Kogi, babu wanda ya fito nuna sha’awar takardar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin APC tukunna.

Share.

game da Author