2023: Mulkin Jigawa ya kamata ya dawo Jigawa ta Arewa-Maso-Gabas a ma’auni na adalci, Daga Ahmed Ilallah

0

Duk da kasancewar wannan batun, batune mai nauyi da wahalar warwarewa, bisa yanayin zamantakewar mu da kuma babancin fahimtar mu akan al’amura irin wannan, kuma ban cika son yin magana irin wannan ba, amma bisa lura da adalcin siyasar Nijeriya, naga ya kamata a tunasar da masu ruwa da tsaki akan wannan batun. Dadi da kari kuma, har gashi an soma buga gangar siyasar 2023.

Jahar Jigawa, wadda aka kirkira a watan Augusta, shekara 1991, a lokacin mulkin soja na General Ibrahim Badamasi Babangida, an kirkireta ne daga tsohuwar Jahar Kano. Jahar Jigawa mai kanan hukumomi 27, Dutse ta kasance babban birnin Jahar. Colonel Olayinka Sule ne gwamna na farko da ya rike jahar, wato Military Administrator.

Jahar Jigawa tana da kimanain al’ummah 5,828,200, a kiyasi na 2016, inji Hukumar Kiddiga ta Kasa wato National Bureau for Statistics NBS, daga cikin wannan kiddiga, al’ummar Jigawa ta Arewa-maso-Gabas, wanda shine daukacin masarautar Hadejia, sune suke da sama da kashi talatin da biyu (32%) na yawan al’ummar wannan jaha, domin suna da yawan al’ummar da ya kai 1,667,7000 a kiyasin Hukumar Kididdiga ta kasa (NBS).

Jahar Jigawa ce, Jaha ta goma wanda take da karfin tattalin arzikin da ba na Mayin-Fetur ba a Nijeriya. An kiyasta cewa, Jahar Jigawa nada karfin arzikin Naira Biliyan Dari Takwas, na abin da take samarwa wato (N800BN GDP Estimate). Noma ne kashin bayan arzikin Jigawa, noma ke samar da sama da kasha 85% na wannan arzikin, kusan tattalin arzikin Jigawa ya ta’allakane a kan noma. Ko a wannan shekarar Jigawa tafi kkowace Jaha noma shinkafa, Ridi da Zoborodo, ta shallake jahohi irin su Kebbi da Taraba a noman shinkafar bana.

Jigawa ta Arewa-maso-Gabas, ke samar da akasarin noman da akeyi a Jigawa, bisa wadatuwar ruwa da albarkar kasar yankin, yankin ne yake da manyan madatsun ruwa na noman rani kamar Hadejia Irrigation Project, da sauran kananan madatsun ruwa da suke a yankin bisa fadamar da Allah ya albarkacin yankin da ita. Kusan a yau Hadejia ce babbar cibiyar kasuwanci a jahar Jigawa, Kanan hukumomin Kaugama, Malam-Madori, Birniwa ke kan gaba wajen noman Ridi da Zoborodo a Jahar Jigawa da ma Nijeriya.

Barrister Ali Sa’ad Birnin Kudu, shine dan asalin Jahar Jigawa na farko da aka zaba a matsayin gwamna, a lokacin mulkin soja na Janar Ibrahim Babangida, an zabe shi a tutar Jama’iyar SDP, Barrister Ali Sa’ad, ya fito ne daga karamar hukumar Birnin Kudu dake Masarautar Dutse, wanda kuma itace Jigawa-ta-Tsakiya a siyasance.

A Shekara ta 1999, lokacin dawowar nijeriya mulkin demokaradiyya, Alhaji Ibrahim Saminu Turaki ne ya zamanto gwamna, a karkashin Jama’iyar APP a wannan lokacin, duk da kasancewar Jama’iyar PDP tafi rinjaye a zaban kanann hukumomi da akayi a wancen lokacin. Ibrahim Saminu Turaki ya fito daga karamar hukumar Kazaure ne, wanda take Jigawa ta Arewa-maso-Yamma. HE Ibrahim Saminu Turaki ya shafe shekara takwas (8) yana mulki, wanda a karshe ya chanja sheka zuwa jama’iyar PDP. A zaben shekara ta 1999, Jigawa ta Arewa-maso-Gabas ce ta bada kasha sittin 60% na tazarar kuri’ar da Gwamna Saminu Turaki ya samu nasarar cin zaben sa a shekara ta 1999.

A shekar ta 2007, Sule Lamido ne, ya samu nasarar zama gwamna a karkashin jama’iyar PDP, wanda ya shafe shekara takwas (8 years) a kan karagar mulki. Governor Sule Lamido ya fito daga Karamar Hukumar Birnin Kudu, wanda take daga yankin Jigawa-ta-Tsakiya.

Governor Muhammad Badaru Abubakar ne ya zamanto gwamna a shekarar 2015, Badaru ya sami rinjayen kuri’a ta sama da kashi 60%, don samun nasarar zama gwamna a karkashin jama’iyar APC, Gwamna Badaru ne ya sake lashe zaben a 2019 a karo na biyu, wanda har yanzu shine ke mulkin wannan jahar.

Bisa da wannan kiddiga, ya zamanto wajibi ga masu ruwa da tsaki a siyasar Jigawa dama Nijeriya da suyi lura da irin wannan yanayin, sukuma duba yanayi na yin daidaito da kuma faminta juna da rabon iko bisa adalci da siyasar zamantkewa.

A tarihin Jigawa, Jigawa ta Arewa-maso-Gabas ne kadai, da basu taba dandana mulkin Jaharsu ba, duka da kasancewar su suke bada kaso mafi yawa a tattalin arzikin jahar Jigawa. Jigawa ta Arewa-maso-Gabas ke bayar da gudunmawa mafi tsoka a duk harkokin siyasar Jihar Jigawa.

A tarihin siyasa da mulki, kasar Hadejia, wanda ita ce Jigawa ta Arewa-maso-Gabas, wadda ta kasance Lardin Hadejia, kafin zuwan mulkin General Yakubu Gawon, Hadejia ita ce Hedikwatar masauratun Kazaure, Daura da Katagun, District Officer wato DO, office dinsa yana Hadejia, a takaice dai Hadejia ce hedikwatar wannan Lardin.

Tabbas lokaci yayi da Yan Jigawa, zasu fahimci junansu, su kara hada kansu, cigaban Jigawa, yau kusan shekaru 20 kenan da zamantowa jihar Jigawa, ta yadda zamu kalli kanmu a matsayin uwa daya uba daya, mu yiwa kanmu adalci.

In mun sake la’akari da yadda ake tafikar da tsarin, duk manyan Jama’iyyu na siyasa a wannan kasar, a kan fidda tsarin sauyin shugabanci da ga wannan yankin zuwa wannan yankin, ba don komai bai sai don daurewar zaman lafiya da kuma cigaban siyasar.

Share.

game da Author