2023: Kungiyar Kiristoci ta fara kaɗa gangar neman Gwamna Yahaya Bello ya zama halifan Buhari

0

Wata ƙungiyar matasan Kiristoci mai suna Christian Youth Leadership Network, ta bayyana cewa Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ne ɗan siyasar da ya fi dacewa ya shugabanci Najeriya, bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala wa’adin mulkin sa cikin 2023.

Ƙungiyar ta bayyana haka a yayin wani taron kwana biyu da ta shirya a Abuja, mai suna “Neman Mafita A Shugabancin Najeriya.”

Wanda shirya taron mai suna Faith Ethes, ta matashi Mai shekaru kamar Yahaya Bello shi ne Najeriya ke buƙata ya shugabance ta a ƙarni na 21. Wanda kuma shi ne zai iya canja alƙiblar siyasar ƙasar nan har a kai gaci.

Ya ce irin Yahaya Bello ake buƙata a ƙasar nan da gaggawa domin ɗora alƙiblar ƙasar nan kan hanyar haɗin kai da daidaituwar zaman tare tsakanin ɓangarori daban-daban na ƙasar nan.

“Idan aka yi nazari da la’akari da irin jagorancin da Gwamna Yahaya Bello ke wa al’ummar Jihar Kogi, za a ga cewa ko shakka babu shi ne ya fi dacewa da shugabancin kasar nan a 2023.”

Ya ƙara da cewa zaɓen da su ka yi wa Bello ya zo daidai da shawarar da tsohon shugaban Najeriya Ibrahim Babangida ya bayar cewa nan gaba kamata ya yi ɗan ƙasa da shekaru 60 za a zaɓa, domin ya gyara ƙasar nan.

Ya ce tun shekaru sama da 30 ko 40 ake cewa matasa su ne manyan gobe ko shugabannin gobe.

“To a yau ya kamata mu ɗauki wannan magana da ake cewa matasa su ne manyan gobe, domin a ba su shugabanci a ga ta su rawar domin ceto Najeriya da warware matsalolin da suka dabaibaye ƙasar.” Inji shi.

Masu jawabai daban-daban sun fito sun kwarzanta Yahaya Bello a matsayin wanda ya cancanta ya zama shugaban Najeriya a 2023.

Tuni dai gwamnan ya fitar da maitar sa a fili ta neman fitowa ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen 2023.

Share.

game da Author