Wani sakamakon bincike da aka gudanar ya lissafo abubuwan da ƴan Najeriya suka fi nema a yanar gizo cikin shekaru 15 da suka wuce.
Bisa ga sakamaon binciken, Menene Soyayya, Yadda ake jima’i, Menene na’ura mai kwakwalwa, Yadda ake rubuta wasikar neman aiki, Menene karatun halitta, Yaya tsadan dala da Naira, Yadda za ka iya kuɗancewa na-da-nan a yanar gizo na daka cikin abubuwan da ƴan Najeriya suka fi nema da bincike akai a yanar gizo.
Waɗanda suke bi musu sun haɗa da binciken labarai da harkokin siyasa daga ingantattun gidajen jaridu.
A fannin nishadi kuma ƴan Najeriya na yawan neman kalmomin wakoki kamar su;
Xxxtentacion Bad Vibes Forever, In Christ Alone lyrics, Brown Skin Girl, All Of Me, Onise Iyanu, Reckless Love, Despacito, Silent Night, Great Is Thy Faithfulness da Ancient Words.
Shahararrun ƴan fina-finan Nollywood da Kannywood da ƴan Najeriya suka nema a ƴanar gizo cikin waɗannan shekaru sun haɗa da,
Mercy Johnson, Funke Akindele, Ini Edo, Odunlade Adekola, Adam A Zango, Iyabo Ojo, Rita Dominic, Angela Okorie, Juliet Ibrahim da Adunni Ade.
Mawakan Najeriya da aka fi nema a yanar gizo sun haɗa da
Burna Boy, Omah Lay, Adekunle Gold, Tope Alabi, Small Doctor, Reekado Banks, Banky W, Frank Edward, 2Face Idibia da Yinka Ayefele.
Mawakan kasashen waje da ƴan Najeriya suka fi nema a yanar gizo
Nicki Minaj, Chris Brown, Cardi B, Ariana Grande, Kanye West, Celine Dion, Meek Mill, Bob Marley, Whitney Houston da August Alsina
Yadda ake haɗa abinci da kayan kwalama
Pornstar martini cocktail recipe, Cake recipe, Pancake recipe, Meat pie recipe, Puff puff recipe, Chocolate cake recipe, Doughnut recipe, Chin chin recipe, Fried rice recipe da Red velvet cake recipe.
Fina-finai na ciki da kasashen waje da aka fi neman su a yanar gizo
Sex and the city movie, The BFG movie, Titanic movie, Black panther full movie, Moana, Frozen 2, Kesari Yoruba movie, Half of a Yellow Sun movie, War room movie da Fifty Shades of Grey movie.
Dabarun hana kiba a jiki
Ketogenic diet, Cambridge diet, Hallelujah diet, Dash diet, Atkins diet, Paleo diet, Diabetic diet, Mediterranean diet, Vegan diet da Ulcer diet
Sannan kuma a Kwallon kafa, an fi neman kungiyoyin kwallon kafa kamar su:
Man U, Real Madrid, Chelsea FC, Arsenal FC, Man City, FC Barcelona, Liverpool FC da AC Milan