Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa ɗorewar zaman tare da kuma haɗin kan Najeriya, kamar zaman aure ne, idan ya ƙi daɗi, sai fa an zauna an sake daddalewa.
Atiku ya yi wannan bayani a wurin ƙaddamar da wani littafin da PREMIUM TIMES ta wallafa.
Littafin dai ya na ƙunshe da maƙalu 60 da ‘yan Najeriya 60 su ka rubuta dangane da mafiya wajen sake gina ƙasaitacciyar Najeriya.
Chido Onumah ne ya gyara tare da yi wa maƙalun ɗauraya, waɗanda ke ɗauke da ƙalubale da mafitar yadda za a iya tabbatar da ɗorewar zamantakewa tsakanin ɓangarorin ‘yan Najeriya daban-daban.
Atiku ya ce ya na mamaki idan ya ji wasu mutane na cewa ba a tattauna batun haɗin kan Najeriya, alhali kuma su ne su ka lalata ƙasar.”
Ya yi magana a kan matsalar tsaro wadda ta ruruta wutar masu tayar da jijiyoyin wuyar neman ɓallewa daga Najeriya.
Wannan tayar dajijiyoyin wuyar neman ɓallewa, wasu da dama na ƙara masa gudu ne saboda zargin da su ke yi cewa wani sashen ƙasar nan ya maida wani sashen saniyar-ware a batun tafiyar da mulkin ƙasar nan.
Sai dai Atiku ya ce za a ci ribar ɗorewa a matsayin ƙasa ɗaya idan ana aiwatar da tsarin adalci da gaskiya ba tare da zargin danne wani ɓangare ba.
“Bai yiwuwa ka riƙa haƙiƙicewa ka na cewa ba za ka yi zaman sulhu da wadda ka ke aure ba, alhali kuma a kullum sai ruruta wutar saɓani ka ke yi tare da matar ka.
“Ana iya kafa ƙasashe da ƙarfin-tuwo, amma ba a iya tilasta jama’a su gina al’umma.” Inji Atiku.
A wurin ƙaddamar da littafin dai Atiku ya bayar da gudunmawar naira miliyan biyu.