Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Sokoto Ali Inname ya bayyana cewa an gano wasu ɗalibai ƴan bautar ƙasa 14 sun kamu da korona a jihar.
Inname ya ce an gano wadannan ɗalibai ne sansanin horas da ɗaliban masu yi wa ƙasa hidima dake jihar.
Ya ce tuni har an killace su gudun kada su sauran abokan zaman su su kamu.
Bayan haka kwamishinan ya ce tun bayan bullar korona a kasar nan gwamnati ta yi wa mutum 19,557 gwajin cutar inda daga cikin mutum 787 na dauke da cutar sannan cutar ta yi ajalin mutum 28 a jihar.
Inname ya yi kira ga mutane da su rika amincewa ana yi musu gwajin cutar da allurar rigakafin Korona domin samun kariya daga kamuwa da cutar.
Mutum 505 sun kamu 3 sun mutu a Najeriya ranar Talata
Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa an samu karin mutum 505 da suka kamu sannan wasu mutum uku sun mutu a dalilin kamuwa da cutar ranar Talata.
Hukumar ta ce an gano wadannan mutane a jihohi 15 da Abuja a kasar nan.
Alkaluman da hukumar ta fitar ya nuna cewa jihar Legas ta samu mutum 273, Rivers-83, Oyo-45, Ondo-23, Cross Rivers-18, Kaduna-13, Ogun -10, Gombe-10, Abuja-8, Ekiti-7, Delta-6, Bayelsa-4, Edo-2, da Neja-1.
Zuwa yanzu mutum 175,000 ne suka kamu, mutum 2,163 sun mutu.
An sallami mutum 165,122 sannan mutum sama da 7,000 na killace a dalilin kamuwa da cutar a kasar nan.
Discussion about this post