ƁARKEWAR KORONA MAI SAURIN KISA: Ta fara kisan-rubdugu a Legas

0

Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Legas sun tabbatar da ɓarkewar korona mataki na 3 mai saurin kisa.

Ministan Harkokin Lafiya Osagie Ehanire da Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas ne su ka bayyana haka a wurare daban-daban a ranar Litinin.

Gwamna Sanwo-Olu ya ce a makon da ya gabata kullum aƙalla sai korona ta kashe mutum shida a Legas, birni mafi bunƙasar kasuwanci a Najeriya.

Shi kuwa da ya ke jawabi, Ministan Lafiya Ehanire ya tabbatar da cewa Najeriya ma kamar wasu ƙasashen Afrika masu yawa, ta na ƙara samun yawaitar ɓarkewar korona mataki na uku, samfurin Delta mai saurin kisa.”

Ya ƙara da cewa, “Dukkan bayanan ƙididdiga na ci gaba da nuna cewa ko shakku da tantama babu, tabbas korona mai zafin da ake gudu samfurin Delta ta ɓarko. Dama kuma tuni mu ke ta gudun ɓarkewar ta.”

Shi kuwa Gwamna Sanwo Olu, ya bayyana a cikin wata sanarwar da ya sanya wa hannu, kuma ya aiko kwafen a PREMIUM TIMES cewa, ya ce, “duk da irin matakai da ƙoƙarin da aka riƙa yi domin hana ɓarkewar wannan korona mai zafin tsiya, to ta dai ɓarke ɗin.

“Yanzu tuni korona mai saurin kisa ta ɓarke. Kamar yadda ta fatan samun sauƙi, to kuma abin da ya faru a yanzu ba mu da wani zaɓi sai dai mu tashi mu yi ƙoƙarin daƙile ta kawai, iyakar ƙarfin mu.

“Ba za mu ce ba mu ƙwarewar yaƙin cutar korona ba. Domin a tsawon watanni 18 da ɓarkewar ta, mun koyi darussa, mun ga ci gaba kuma mun ci karo da cikas ko koma-baya. To kuma sai mu tashi tsaye domin tabbatar da cewa wannan korona zango na uku ita ce zangon ƙarshe.

Da ya ke bayanin irin kisan da ta ke yi, Sanwo-Olu ya ce cikin 2020 a Legas kaɗai mutum 64,032 sun kamu da cutar korona, amma mutum 56,336 sun murmure.

Sai dai kuma ya ce har yanzu ana jiyyar mutum 2,755, yayin da aka kwantar da mutum 5,029 a cibiyoyin kula da masu korona daban-daban.

Batun kisan da cutar ke yi kuwa, ya ce, “ta kashe mutum 390 a Legas, daga ciki kuma 30 wannan korona ce matakin Delta ta halaka su.

“Tun daga makon da ya gabata, aƙalla kullum cutar na kashe mutum shida a Legas.”

Share.

game da Author