Ƴan bindiga sun sace mutum 60 a Rini jihar Zamfara

0

Kwamishinan Yada Labarai na jihar Zamfara, Ibrahim Dosara ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun sace mutane akalla 60 a kauyen Rini, dake Karamar Hukumar Bakura jihar Zamfara.

Dosara ya kara da cewa dalilin da ya sa hare-haren ‘yan bidiga da sace mutane yayi tsanani yanzu a jihar Zamfara, shine don luguden wuta da rundunar sojojin Najeriya ke yi wa ‘yan bindigan a cikin dazukan dake kewaye da su, musamman sojojin sama.

Kwamishina Dosara ya bayyana haka a lokacin da yake hira da talbijin din TVC ranar Juma’a.

” Wuta da ‘Yan bindiga suke sha daga rundunar Sojin Saman Najeriya ya sa garkuwa da mutane yayi tsanani a jihar Zamfara.

Idan ba a manta ba a Karamar Hukumar Bakura ne yan bindiga suka yi garkuwa da daliban makarantar koyon aikin noma wanda har yanzu suna tsare a hannun ‘yan bindigan.

A wani bidiyo da ‘yan bindigan suka fitar a cikin wannan makon, an nuno daliban wannan makarant zaune sun kira ga gwamnati ta kawo musu dauki a taimaka a biya kudin fansan da suke nema idan ba haka ba za su kashe su.

Maharan sun baiwa gwamnatin Zamfara wa’adin awa 24 su biya kudin ko kuma su kashe su.

Sai dai har yanzu ba a samu rahoton ko gwamnati ta amsa bukatun yan bindiga ba.

Share.

game da Author