Ƴan bindiga sun sace ɗaliban makaranta a Zamfara, sun kashe jami’an tsaro 4

0

A ci gaba da fama da rashin tsaro da yayi wa jihar Zamfara da yankin Arewa maso gabashin Najeriya rawani, ƴan bindiga sun afka makarantar koyon aikin Noma dake garin Bakura, inda suka sace ɗalibai da wasu daga cikinsu nbmalaman makarantar.

Rajistaran kwalejin Aliyu Bakura ya bayyana cewa maharan sun sace ɗalibai 15 da wani malami da matar sa.

” Ƴan bindigan sun shigo makarantan ɗauke manyan makamai. Sun kashe jami’an tsaro hudu har da ƴan sanda.

Har yanzu akwai ɗalibai da dama dake tsare hannun ƴan bindiga ba a sako su ba.

A jihar Neja, har yanzu ƴan makarantan Islamiya akalla 200 na can tsare hannun ƴan bindiga ba a kai ga ceto su ba.

Wannan dalili ya sa dole gwamnatin Kaduna ƙarkashin Nasir El-Rufai ya ɗage komawa makarantu a jihar har sai an samu saukin hare-haren ƴan bindiga.

Share.

game da Author