Ƴan bindiga sun kutsa makarantar Sojoji NDA, a Kaduna sun kashe sojoji biyu, sun sace babban jami’in soja

0

Rahotanni sun tabbatar da cewa mahara sun kutsa Makarantar Horas da Hafsoshin Sojoji ta NDA a Kaduna, inda su ka kashe sojoji biyu kuma su ka gudu da wani jami’in soja babba guda ɗaya.

Ganau ya ce ‘yan bindigar su na da yawa, domin gungu ne su ka yi su ka darkaki sojojin, tsakar dare kafin wayewar garin Talata.

Baya ga waɗanda su ka kashe da babban sojan da su ka gudu da shi, sun buɗe wuta inda kuma su ka raunata wasu, da a yanzu haka ke kwance a asibitin NDA ana kula da lafiyar su.

Lamarin ya zo bayan wani rahoton sirri da ya tabbatar da cewa Boko Haram sun kafa tuta a Dajin Afaka, wanda ke kusa da NDA da kuma Filin Jirgin Sama na Kaduna.

Harin ya zo kwana ɗaya bayan ‘yan bindiga sun yi wa mutum 10 yankan-rago kuma sun arce da mutum 70 a ƙauyen Goran Namaye cikin Ƙaramar Hukumar Maradun, Jihar Zamfara.

Share.

game da Author