A ci gaba da fama da rashin tsaro da yayi wa jihar Zamfara da yankin Arewa maso gabashin Najeriya rawani, ƴan bindiga sun kashe wasu mutum 13 ciki har da maijego da jaririnta.
A daidai ƴan bindiga suna aikata wannan mummunar kisa da suka kai a Maru, A Bakura wasu bangaren ƴan bindiga na sace ɗaliban kwalejin koyan ayyukan gona.
Wani basarake a karamar hukumar Maru ya shaida wa wakilin mu cewa maharan da yawa daga cikin waɗanda aka sace wasu daban sun gudu da ga ƴan bindigan a lokacin da suke nausawa daji da su.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda ƴan bindiga suka afka makarantar koyon aikin Noma dake garin Bakura, suka sace ɗalibai da wasu daga cikinsu malaman makarantar.
Rajistaran kwalejin Aliyu Bakura ya bayyana cewa maharan sun sace ɗalibai 15 da wani malami da matar sa.
” Ƴan bindigan sun shigo makarantan ɗauke manyan makamai. Sun kashe jami’an tsaro hudu har da ƴan sanda.
Har yanzu akwai ɗalibai da dama dake tsare hannun ƴan bindiga ba a sako su ba.
A jihar Neja, har yanzu ƴan makarantan Islamiya akalla 200 na can tsare hannun ƴan bindiga ba a kai ga ceto su ba.
Wannan dalili ya sa dole gwamnatin Kaduna ƙarkashin Nasir El-Rufai ya ɗage komawa makarantu a jihar har sai an samu saukin hare-haren ƴan bindiga.
Discussion about this post