Ƴan bindiga sun buɗe wa motocin jami’an tsaron da ke yi wa matafiya jagora zuwa Ɗansadau daga Gusau

0

Ƴan bindiga sun bude wa motocin jami’an tsaro da ke yi wa matafiya jagora zuwa garin Ɗansadau, sannan suka cinna wa wata motar mai wuta.

Wasu mazauna garin Ɗansadau sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa ƴan bindigan sun sha alwashin sai sun hana mutane sakat a wannan yanki saboda kin saida musu da kayan abinci da mutanen garin suka yi.

” Yanzu dole sai an yi wa matafiya jagora zuwa garin Ɗansadau daga Gusau idan ba haka ba kuwa tafiyar bashi yiwuwa.

” Maharan sun yi wa motocin kwantar ɓauna ne, kafin su ankare sun buɗe musu wuta.

Share.

game da Author