Mahukuntan Amurka sun horas da masu bincike har mutum 50 ‘yan Najeriya. An koya masu dabarun daƙile damfara a hada-hadar zamani ta ‘cryptocurrency’.
Wannan bayanin na ƙunshe ne a cikin wani bayani da Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta bayyana a cikin shafin ta na Twitter, a ranar Alhamis.
Horaswar da aka yi masu a tsarin daga-nesa, wato ‘virtual’, ta ta’allaƙa ne kacokan a kan yadda ake gane harƙalla a tsarin hada-hadar ‘bitcoin’, wato ‘cryptocurrency’.
An gudanar da horaswar da haɗin-guiwar Hukumar Binciken Amirka (FBI), Ofishin Jakadancin Amirka da ke Kenya, Addis Ababa, Ofishin Jakadancin Amirka da ke Najeriya da kuma Shirin Gwamnantin Amirka kan yaƙi da hada-hada da cinikin muggan ƙwayoyi a duniya.
Haka kuma waɗanda aka bai wa horon su 50 ‘yan Najeriya, jami’ai ne da su ka haɗa da masu shigar da ƙara ko masu gabatar da ƙarar masu aikata laifuka, waɗanda za su iya gabatar da masu damfarar ‘cryptocurrency’ a kotu.
Hada-hadar ‘bitcoin’ dai tsari ne da ake sayen ƙwandalar zamani, ta yadda za a iya saye da sayarwa da kuɗaɗen. Kuma ana yin hada-hadar don riba.
Premium Times ta buga labarin yadda darajar ‘Bitcoin’ ta haura dala 50,000 bayan karyewar da ƙwandalar ta yi cikin watan Afrilu.
Darajar ƙwandalar hada-hadar ƙuɗaɗe ta ‘Bitcoin’ ta sake tashi zuwa sama da dala 50,000 a duniya, a ranar Litinin, bayan karyewar martabar kuɗin, watanni uku da su ka gabata.
Ƙwandalar a ranar Litinin wajen ƙarfe 2:20 na yamma ta kai dala 50,274.68 daidai agogon Najeriya.
Hakan ya faru ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin cewa Amirkawa za su ƙara narka kuɗaɗe hada-hada, ta yadda za a ƙara samun riba.
‘Bitcoin’ ya ƙara daraja da kashi 2.84 cikin sa’o’i 24. Wato kashi 6.25 kenan a kowane mako.
Yayin da ƙarfin jarin ‘Bitcoin’ a kasuwannin hada-hada a yanzu ya kai dala biliyan 31,449,905,210.17. Wato ya ƙaru kenan da kashi 8.49 bisa adadin sa na baya.
Cikin watan Afrilu ne dai darajar hada-hadar amfani da ‘Bitcoin’ ta yi ƙasa warwas, inda a ranar 14 Ga Afrilu ya yi ƙasa, bayan ya kai dala 64,863.10.
Shi ma farashin cyrptocurrency na Ether ya tashi da kashi 2.8, wato ya kai dala 3,337.
Hakan na nufin ya tashi da kashi 91 bisa 100, bayan ya yi ƙasa zuwa dala 1,740 a cikin watan da ya gabata.
Kafofin yaɗa labarai a Turai sun bayyana cewa ƙwandalar cyrptocurrency ta samu tagomashin farfaɗowa, bayan kamfanoni da cibiyoyi irin su PayPal sun amince su bar kwastomomin su yin hada-hadar kuɗaɗen.
Sannan kuma za su amince wa kwastomomin su na Birtaniya su saya ko su sayar da ‘bitcoin’ da sauran nau’ukan ƙwandalolin ‘cryptocurrency’ daga wannan mako da aka shiga a yau.
Discussion about this post