ƘURUNƘUS: Buhari ya sa wa Dokar Rabon Arzikin Man Fetur (PIB) hannu, ya yi biris da ƙorafe-ƙorafen masu raina kashi 3% bisa 100%

0

A ranar Litinin ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu kan Ƙudirin Dokar Rabon Arzikin Mai ta Ƙasa, wanda hakan na nufin ƙudirin ya zama doka.

Ƙudirin ya shafe shekaru 10 a gaban Majalisa ana dambarwa da kwan-gaba-kwan-baya a kan sa. Amma a ranar 15 Ga Yuli, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya sa masa hannu, bayan ƙudirin ya sha tirjiya da zamiya a majalisun biyu.

Sai dai kuma Buhari ya sa wa ƙudirin hannu tare da yin biris da ƙorafe-ƙorafen da al’ummomin da ake haƙo man fetur su ka yi a kan ƙudirin.

Al’ummomin dai a ta hannun gwamnonin su da wakilan su da kuma dattijon yankin su na Neja-Delta, Edwin Clark, sun raina kashi 3% bisa 100% na rarar ribas da aka ce za a riƙa warewa domin bunƙasa yankunan ta hanyar ilmi da gurɓatar yanayi da sauran su.

PREMIUM TIMES Hausa ta bi diddigin yadda dambarwar ta kasance tun daga lokacin da aka kafa kwamitocin bin-diddigin ƙudirin domin a sa masa hannu a cikin wannan shekarar.

Su dai al’ummar yankin Neja-Delta sun nemi a riƙa ba su kashi 10% bisa 100%. Ko kuma kashi 5% bisa 100%, kamar yadda Majalisar Tarayya ta amince a lokacin da ta miƙa wa Majalisar Dattawa Ƙudirin bayan ta kammala aikin ta.

Sai dai kuma a Majalisar Dattawa an zaftare adadin kason da za a riƙa basu, daga kashi 5% zuwa kashi 3% kacal, laamrin da ya tada ƙura kamar yadda PREMIUM TIMES Hausa ta tattaro wa masu karatu yadda lamarin ya wakana a baya-bayan nan.

Idan ba a manta ba, a daidai lokacin da Gwamnonin Neja-Delta da da sauran al’ummar yankin ke ƙorafe-ƙorafe, Ministan Harkokin Neja-Delta Godswill Akpabio, ya roƙi Majalisar Dattawa ta yi biris da ƙorafen-ƙorafen jama’a, ta miƙa wa Buhari ƙudirin ya sa hannu, a wuce wurin.

Ministan Harkokin Neja-Delta, Godswill Akpabio, ya shawarci Majalisar Dattawa cewa ta daina tsayawa sauraren ƙorafe-ƙorafen jama’a a kan Kudirin Dokar Raba Ribar Fetur, ta miƙa wa Shugaba Buhari gyaran da su ka yi, shi kuma ya sa hannu ba tare da ɓata lokaci ba.

Ya ce a daina tsayawa sauraren bimbinin al’ummar yankin da ake haƙo fetur, a saki dokar kawai ta fara aiki, a wuce wurin.

Idan ba a manta ba, Dattijo kuma jagoran Yankin Neja Delta Edwin Clerk, ya yi barazanar cewa za su hana haƙo ɗanyen mai a Najeriya saboda ƙudirin dokar ribar fetur ta fifita wasu jihohin Arewa kan jihohin da ake haƙo mai.

Dattijo mai faɗa a ji a yankin Neja Delta, ya bayyana cewa za su hana kamfanonin haƙo ɗanyen mai su ci gaba da aiki a yankin Neja Delta, matsawar dai ba a dawo da kudirin raba ribar man fetur da Majalisa za ta gabatar ba.

Clerk ya ce ‘Yan Majalisar Dattawa da na Tarayya sun raina wa al’ummar Yankin Neja Delta wayau, saboda sun soke kason kashi 10 bisa 100 da za a riƙa ba Neja Delta, su ka maida shi kashi 3 bisa 100, sannan su ka lafta wa wasu jihohin Arewa har kashi 30 bisa 100.

Ya kira wannan ƙudiri da cewa, ƙudirin iya shege ne da shaiɗanci da kuma tantagaryar rashin adalci.

“Lokacin Daina Yi Mana Mulkin Mallaka Ya Yi” -Edwin Clerk

“Mu na gargaɗin cewa jama’ar Neja Delta da an kai su bango. Tutar ta isa haka. Mun gaji da irin mulkin da ake yi mana mai kama da mulkin mallaka, wanda ‘yan uwan mu da abokan mu ‘yan Arewa ke yi mana.

“A yau ragamar harkokin fetur a ƙasar nan ta na hannun ‘yan Arewa, duk da dai harkokin yaƙi man kamfanonin ƙasashen Turai ne ke gudanarwa a madadin Gwamnatin Tarayya.” Inji Clerk.

Dattijo Clerk wanda shi ne jagoran wata ƙungiyar kare muradun Neja Delta, PANDEF, ya ce shi da sauran ɗaukacin dukkan ‘yan Neja Delta sun ƙi amincewa da kason cikin cokali na kashi 3 bisa 100 na ribar mai da za a ba yankin Neja Delta sa kuma kashi 5 cikin 100 da aka ware wa NNPC Limited da za a rika bai wa al’ummar yankin da ake haƙo man.

“Idan ba a yi mana haka ba kuwa, to ya zama tilas mu tashi tsaye mu fito mu ƙwaci haƙƙin mu da tsiya-tsiya. Kuma sai mu hana kamfanonin haƙo ɗanyen mai ci gaba da aikin haƙar mai a yankin mu.”

Shi kuwa Akpabio cewa ya yi “wannan ƙudiri da tun shekaru 20 ya ke jibge a Majalisar Tarayya da ta Dattawa. Ina magana ne a madadin jama’ar Neja Delta. Kada fa su jangwalo abin da zai ƙara kawo wa wannan ƙudiri cikas. Ko kashi nawa za a ba mu, ko 3, 4 ko biyar kawai mu haƙura mu karɓa. Daga baya mu koma mu nemi ƙari.”

PREMIUM TIMES ta buga matsayar Gwamnonin Kudu a kan matsalar tsaro, gyaran kundin mulki da Kudirin Dokokin Raba Ribar Fetur kamar haka:

Bayan kammala taron da Gwamnonin Yankin Kudu gaba ɗayan su suka halarta a Legas ranar Litinin 5 Ga Yuli, 2021, sun bijiro da wasu buƙata, sharuɗɗa da kuma matsayar su a kan baturuwan da su ka bijiro da su.

1. Makomar Najeriya: Sun yarda cewa Najeriya ta ci gaba da kasancewa dunƙulalliyar ƙasa ɗaya, amma a bisa haɗin kai, kaunar juna, gaskiya da gaskiya, adalci da kuma raba-daidai gwargwado na arzikin ƙasa da muƙamai.

2. Tilas Ɗan Kudu Zai Yi Shugabanci A Zaɓen 2023: Gwamnonin Kudu sun yarda cewa a riƙa gudanar da ingantacciyar siyasa nagartacciya, ba tare da maida wani ɓangare saniyar-ware ko gugar-yasa ba. A kan haka, sun cimma matsayar lallai ɗan kudu ne zai yi shugabancin Najeriya a zaɓen 2023. Sun kuma amince a riƙa yin tsarin karɓa-karɓa tsakanin kudu da Arewa.

3. Matsalar Tsaro:
a. Sun jinjina wa jami’an tsaro, sun yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda su ka rasa rayukan su. Kuma sun yi jaje ga waɗanda aka raunata.

b. Sun jaddada buƙatar a bar kowace jiha ta kafa ‘yan sandan ta.

c. Tilas idan jami’an tsaro za su yi wani aikin kame ko farmaki a wata jiha, to fara sanar da gwamnan jihar tukunna.

d. Gwamnonin Kudu sun yi tir da abin da su ka kira nuna fifiko da nuna bambanci wajen yadda gwamnatin tarayya ke daƙile wani ba’arin masu laifi ta kauda kai ga wani ɓangare na masu laifin. Sun ce duk wanda jami’an tsaro za su kama, to a riƙa bin matakin da doka ta gindaya, ba tare da danne haƙƙin ɗan Adam ba.

e. Sun aza ranar 1 Ga Satumba, 2021 ta kasance ranar da za su fara aiki gadan-gadan da dokar haramta karakainar kiwon shanu sakaka a jihohin kudu baki ɗaya.

f. Sun ce lallai kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke cirewa daga Aljihun Gwamnatin Tarayya domin bai wa Hukumar Gidauniyar ‘Yan Sanda, a riƙa raba kuɗaɗen har da gwamnatin jihohi domin su ma su yi amfani da kuɗaɗen wajen daƙile matsalar tsaro.

4. Kudirin Dokar Rabon Ribar Fetur (PIB):

a. Sun jinjina wa Majalisar Dattawa da ta Tarayya dangane da ci gaban da aka samu.

b. Sun raina, kuma sun ƙi amincewa da kashi 3% bisa 100% ɗin da aka ware masu na kuɗin, maimakon kashi 10% bisa 100% da Majalisar Tarayya ta rattaba amincewa a riƙa biya.

c. Gwamnonin Kudu sun ƙi amincewa da riƙa cire kashi 30% na ribar fetur don a riƙa kashe ta wajen aikin neman mai a wasu jihohi.

d. Sun kuma yi fatali da tsarin mallakar kamfanin NNPC Limited. Sun ƙi yarda kamfanin ya kasance ƙarƙashin Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe bisa kulawar Hukumar NSIA. Sun ce ai gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi duk su na da haƙƙi a ciki su ma.

5. Sun ƙi amincewa da soke tsarin amfani da kwamfuta wajen aikawa da sakamakon zabe.

6. Kungiyar Gwamnonin Kudu ta amince Jihar Lagos ta zama hedikwatar ƙungiyar ta dindindin. Kuma sun gode da irin kyakkyawar tarba da ɗaukar nauyin taro da Gwamnan Jihar Legas ya yi masu.

Share.

game da Author