Ƙasashen Turai fatali su ke yi da fiye da kashi 76% na amfanin gonar da ake nomawa a Najeriya -FOA

0

An bayyana cewa Ƙasashen Tarayyar Turai na fatali da fiye da kashi 76% bisa 100% na kayan gonar da ake nomawa a Najeriya, saboda ba su cika ƙa’idojin da su ka kamata su cika kafin a karɓe su.

Daraktan Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), Mojisola Adeyeye ce ta bayyana haka a Abuja.

Adeyeye ta yi wannan bayani a lokacin wata hira da ita a gidan talabijin na Channels, a ranar Talata.

Ya yi bayanin ne dangane da matakan da ake ɗauka domin inganta kayan abincin da ake fitarwa a ƙasashen Turai.

“Kashi 76% bisa 100% na kayan gonar mu duk fatali ƙasashen Turai ke yi da su. Kuma hukumar mu ta NAFDAC ce aka gaggauta sanarwa cewa an ƙi karɓar kayan abincin.” Inji Adeyeye.

Ta ce baya ga asarar maƙudan kuɗaɗen da ake yi, to kuma kare martaba da darajar Najeriya a idon duniya, abu ne mai muhimmanci matuƙa.

“Sai mun ƙara tashi tsaye sosai mun yi aiki tuƙuru domin mu nuna muna kaunar ƙasar mu. Ta haka ne ba za mu riƙa zubar wa Najeriya martaba da mutunci ba a idon duniya.

Ta ce “rai na ya na ɓaci matuƙa idan na ga irin yadda ake ƙin sayen kayan abincin Najeriya a ƙasashen Turai. Saboda na san irin kuɗin da mai kayan abincin zai yi asara.

“Zuciya ta na ɓaci kuma tausayi kan kama ni idan na ga irin yadda ake fitar da kayan abinci daga Najeriya zuwa ƙasashen Turai sannan a ƙi amincewa da su. Saboda mutum ya sha wahala, wataƙila ma ramcen kuɗin ya karba.” Inji ta.

Sai dai kuma ta ce a yawancin lokutan laifin masu fitar da kayan ne, domin sau dawa su na kaucewa da bijire wa ƙa’idojin da ƙasashen da ke ƙin karɓar kayan na su su ka gindaya.

Share.

game da Author