Ƙasashen Afrika ta Yamma za su yi amfani da tsarin sa ido a zaɓe na INEC — Farfesa Yakubu

0

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ƙasashe da dama a yankin Afrika ta Yamma sun nuna sha’awar su kan nazari tare da kwaikwayon hanyoyin zamani da ta fito da shi don sa ido kan yadda ake gudanar da zaɓe don su ma su yi aiki da shi.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a ranar Juma’a a wajen buɗe taron ƙara wa juna sani na kwana biyu kan ”inganta tsarin gudanarwa na cibiyar sa ido kan zaɓe da bada tallafi (EMSC)” wanda aka a Keffi, Jihar Nasarawa.

Yakubu ya ce cibiyar EMSC ta zama wani muhimmin kayan aiki wajen sanya ido, aiwatarwa da gudanarwa a tsare-tsare da ayyukan zaɓe a Najeriya.

Ya ce lokacin da aka ƙaddamar da hukumar a ƙarƙashin sa a karon farko a cikin Nuwamba 2015, ƙudirin ta shi ne ta ɗora kan hukumar da ta gabace ta (2010-2015) wajen gina tsare-tsare don samun cigaba tare da ingantaccen tsarin gudanar da zaɓe.

Yakubu ya ce ƙudirorin ba wai kurum don su magance matsalolin da aka fuskanta a lokacin manyan zaɓuɓɓukan shekarun 2011 da 2015.

Ya ce wata manufar tata ita ce a fito da tsare-tsare masu inganci da aka gina kan ilimi waɗanda za su magance matsalolin da aka samu a cikin 2019, sannan a ci gaba da tallafa wa ƙoƙarin da hukumar ke yi wajen tsarawa da gudanarwa da kuma gudanarwar zaɓe.

”Daga nan, a cikin shekaru masu zuwa, hukumar ta ci gaba da faɗaɗa iyakokin ta na gudanar da zaɓe ta hanyar fito da sabbin hanyoyi da tsare-tsare bisa ilimi. Ita EMSC ta na daga cikin irin waɗannan sabbin hanyoyin.

”Ta wannan hanyar, EMSC ta kan sama wa hukumar bayanan da ta ke buƙata don ɗaukar matakan kauce wa matsaloli ko barazana ga zaɓe.”

Yakubu ya ƙara da cewa a shirye-shiryen da ake yi na babvan zaɓrn 2019, a bayyane ya ke ga INEC cewa ya kamata a samar da wani tsari na sammun gargaɗin wuri, sa ido da aiwatarwa.

Ya ce saboda haka INEC ta karɓi shawarwarin ‘yan Kwamitin Tsarin Aikin Zaɓe na babban zaɓen 2019 (EPPC) don a haɗe hanyoyi uku na sa ido na hukumar zuwa abu guda ɗaya da za a kira EMSC.

Ya lissafa waɗannan hanyoyin kamar haka: tsarin gudanarwa na zaɓe (Election Management System, EMS), gudanarwar barazana ga zaɓe (Electoral Risk Management, ERM) da cibiyar tallafa wa aikin zaɓe (Election Operations Support Centre, EOSC).

Ya ce, “Cibiyar EMSC ta taimaka wa hukumar matuƙa wajen gudanar da aikin zaɓe.

”A matsayin wata shaida ta hoɓɓasan ta a matsayin wani makamin gudanar da zaɓe, ƙasashe da dama a yankin Afrika ta Yamma da ma wasu sun nuna sha’awar su ta yin nazari tare da kwaikwayon wannan tsarin domin su yi amfani da shi.

” Hukumomin zaɓe a Etofiya da Malawi har sun fara duba yiwuwar yin amfani da wasu sassa daga cikin tsarin mu wajen gudanar da zaɓuɓɓukan su.

”EMSC za ta iya kasancewa wata gudunmawa ta INEC (da ma Nijeriya) ga aikin gudanar da zaɓe na duniya.”

Yakubu ya ce masanan farko da INEC su na buƙatar su ci gaba da faɗaɗa iyakokin tsarin su, su ƙarfafa su, su magance matsalolin su kuma su faɗaɗa su wajen gudanarwa tare da aiwatar da zaɓuɓɓukan.

”Da yake an yi amfani da shi a babban zaɓen 2019, tabvas hukumar ta ga alfanun sa da kuma matsalolin shi.

”Akwai buƙatar a ƙarfafa alfanun tare da haɓaka shi a yayin da ake warware matsalolin da ake hangowa kafin babban zaɓen 2023, wanda ya rage kwana 560 kacal.”

Shugaban ba INEC ya ƙara da cewa don haka amfanin wannan taron ƙara wa juna sanin ya na da yawa ga EMSC da hukumar.

Ya yi kira ga mahalarta taron da su yi aiki tuƙuru a lokacin taron, su fito da sabbin hanyoyin inganta EMSC, su warware dukkan ƙalubalen da ta ke fuskanta kuma su fito da cikakkun hanyoyin tafiyar da ayyukan ta.

”Tilas ne a sake mata garambawul domin ta aiwatar da manyan haƙƙoƙin da su ka rataya a wuyan ta na samar da tsarin gargaɗin wuri, a gano barazana da hanyoyin sa ido wajen gudanar da ayyukan zaɓe.

“(Tilaa ne) a sake mata fasali don tabbatar da samun ingantattun bayanai a bai wa hukumar kan dukkan ayyukan da ke da tasiri kai-tsaye kan zaɓuɓɓuka.”

Mista Hamza Fassi-Fihr, Kodinetan Aiki a cibiyar tallafin zaɓe ta Turai (European Centre for Election Support, ECES), ya ce sa ido kan tsare-tsare ya na da muhimmanci ga samun nasarar kowane irin tsari kuma sadaukar da kai ga rabbatar da tsare gaskiya.

Fassi-Fihri, wanda Dakta Isiaka Yahaya, babban jami’in gudanarwa na ECES, ya yaba wa ƙoƙarin da INEC ke yi wajen tabbatar da kyakkyawan tsarin sa ido kan harkar zaɓe da haɓaka ingancin zaɓe ta hanyar sabon makami.

”A bayyane ya ke cewa tsarinvEMSC ya zo kenan a matsayin wani muhimman sashe na tsarin gudanar da zaɓe na Nijeriya kuma tsarin da za a kai wa dukkan EMBS da ke yankin Afrika da sauran ƙasashe.”

Share.

game da Author