A ranar Litinin farashin naira ya ƙara faɗuwa warwas, inda ta kai adadin da ba ta taɓa kaiwa ba, zuwa Dala 1 daidai da naira 527.
A ranar Juma’a dai an tashi daga kasuwar ‘yan canji inda Dala 1 ke daidai da naira 524, kamar yadda shafin tattara farashi da bayanan kasuwar ‘yan canji na yanar gizo, wato abokiFX.com ya tabbatar a Legas.
Wani ɗan canji a garin Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom, mai suna Shaibu Isa, ya danganta ƙarancin Dala a kasuwa da matakan da CBN ya ɗauka na daina sayar da kuɗaɗen ƙasashen waje ga masu canji.
Cikin ƙarshen makon jiya ne wannan jarida ta bada labarin yadda Dala na ci gaba da gwabzar bakin naira a kasuwar ‘yan canji, yanzu ta kai naira 524.
Darajar naira na ci gaba da taɓarɓarewa a tsakanin kuɗaɗen ƙasashen waje, ta yadda a ranar Juma’a sai ta kai ana sayen dala 1 naira 524.
Karo na uku kenan a jere kowace rana dala ta riƙa tashi, darajar naira kuma na karyewa.
An tashi kasuwa ranar Alhamis an sayar da dala ɗaya kan naira 522.
Haka lamarin yake a farashin gwamnati, inda aka sayar da dala ɗaya naira 412 a yammacin ranar Juma’a, alhali kuma naira 410.88 aka sayar da ita.
Farashin dala ya yi sama tun bayan da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya daina sayar wa ‘yan canji kuɗaɗen waje.
Haka kuma CBN ya daina bayar da lasisin amincewa kamfanonin hada-hadar canji yin canjin su na kuɗaɗen waje.
Premium Times ta buga labarin yadda dala ta tashi zuwa Naira 517, bayan da CBN ya yi sanarwar daina sayar wa ‘yan canji kuɗaɗen waje.
Kuma jaridar ta yi cikakken rahoton yadda CBN ya maida wa kamfanonin masu canji ko musayar kuɗaɗen waje naira miliyan 35 da kowane kamfanin canji (BDC) ya ajiye, kafin bankin ya riƙa sayar masa da kuɗaɗen ƙasashen waje.
Haka kuma CBN zai biya kamfanonin canjin, waɗanda aka fi sani da ‘Bureau De Change’ kuɗaɗen su da ya karɓa ya riƙa yi masu rajistar lasisin amincewa su riƙa yin canjin kuɗaɗen ƙasashen waje.
Wata sanarwa da Daraktan Tsare-tsaren Kuɗaɗe na CBN, Ibrahim Tukur ya sa wa hannu, ta nuna cewa CBN za ta biya su kuɗaɗen ne bayan da ya daina sayar da dala da sauran kuɗaɗen waje ga masu ‘yanji ko ‘yan kasuwar tsaye, wato ‘yan BDC.
CBN dai ya riƙa karɓar naira miliyan ɗai-ɗai a wurin kamfanonin BDC domin yi masu lasisi, sai kuma naira miliyan 35, matsayin adadin kuɗay da kowane ɗan canji mai rajista zai ajiye a CBN, a matsayin yi masa rajista da kuma riƙa sayar masa da kuɗaɗe.
An dai umarci duk waɗanda su ka biya kuɗaɗen su hanzarta rubuta takardar neman a maido masu kuɗaɗen da su ka biya.
Sannan kuma za su cika fam tare da aika lambar takardar shaidar sun biya kuɗaɗen da kuma lambar asusun bankin da mutum yi amfani da ita ya tura wa CBN kuɗaɗen.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin dalilin da ya sa CBN ya daina sayar wa ‘yan canji kuɗaɗen ƙasashen waje.
Babban Bankin Najeriya CBN ya bada sanarwar daina sayar wa ‘yan canji kuɗaɗen waje kai-tsaye.
Shugaban Bankin CBN, Godwin Emefiele ne ys sanar da haka a ranar Talata a Abuja, bayan taron kwanaki biyu da Majalisar Tasarifin Tsare-tsaren Kuɗaɗe ta CBN ta gunadar.
Emefiele ya ce daga yau CBN zai riƙa sayar da dala d sauran kuɗaɗen waje ga bankunan kasuwanci kaɗai, ba ga ‘yan canji ba.
“Kuma CBN daga yau babu ruwan sa da shiga sha’anin yi wa kamfanonin ‘yan canji rajista.”
Ya ce wannan tsari da su ka ɗauka zai taimaka ƙwarai wajen ƙara wa naira ƙarfi da daraja a gaban idon kuɗaɗen ƙasashen waje.
CBN ya ce ya lura ana amfani da ‘yan canji ana karkatar da kuɗaɗen da ya kamata a ce an zuba su ne a jarin bunƙasa kasuwanci da tattalin arzikin cikin gida.
Daga nan sai ya ce duk mai son kuɗaɗen waje ya je wurin bankunan kasuwanci ya riƙa saye.
Sannan ya gargaɗi bankuna cewa duk wanda ya haɗa baki da ‘yan canji, za a yi masa hukuncin da sai ya yi da-na-sani.
Ya kuma gargaɗi ƙungiyoyin ƙasashen ƙetare waɗanda ya zarga da karkatar da kuɗaɗe ta hannun ‘yan canji, cewa su daina. Duk wanda aka kama, za a kai rahoton sa a gwamnatin ƙasar su.
PREMIUM ta buga labarin yadda wani masanin hada-hadar kuɗaɗe ya roƙi Bankin CBN ya rataya wa naira layar laƙanin hana ta firgita idan ta yi ido-biyu da dala a kasuwannin hada-hada.
Wani masanin ƙabali da ba’adin harkokin kuɗaɗe, Okechukwu Unegbu, ya roƙi Babban Bankin Najeriya (CBN) ya lalubo hanyoyin da zai saisaita tsadar kayan abincin da kayan masarufi ta hanyar dakatar da yawan farfaɗiya da faɗuwar ‘yan bori da naira ke yi a kasuwannin hada-hada na ciki da wajen ƙasar nan.
Okechukwu ya ce tsadar kayayyaki na ƙara tsananta cikin ƙasa, saboda darajar naira na ci gaba da taɓarɓarewa, sannan kuma a waje ko cikin gida duk inda naira ta yi ido-biyu da dala, sai ta fara karkarwa ta na firgita.
Okechukwu wanda shi ne tsohon Shugaban Ƙungiyar Mashahuran Masana Harkokin Kuɗaɗe na Cibiyar CIBN ta Najeriya, ya bada wannan shawara ce a ranar Lahadi, a wata tattaunawa da manema labarai a Abuja.
Ya ƙara da cewa yawan karyewar darajar naira da ake fuskanta abin damuwa ne, domin yanzu akwai wasu sinadarai da su ka kamata a yi amfani da su, wajen ƙara wa naira ƙarfi ta daina yawan firgita ko faduwar-‘yan-bori.
“Ya kamata Kwamitin Tsare-tsaren Ka’idojin Hada-hadar Kuɗaɗe na CBN ya yi nazarin shingayen da za a gindaya wa naira, matsayin kan iyakar da za a hana ta tsallakewa, kamar yadda bankin ya yi sau shida a baya.
“Har yanzu tsadar rayuwa da tsadar kayayyaki na hauhawa a Najeriya. Ƙuɗaɗen ruwan da bankuna ke bayarwa kuma sai hawa-da-sauka su ke yi. Sannan kasuwar canjin kuɗaɗen waje kuwa a nan ne aka fi yi wa naira laga-laga ko da kallo ta je, ballantana ta je cin kasuwar.
“Yanzu kusan naira 500 ce daidai da dala 1. A Najeriya idan ka na da naira 500, za ka iya cin abinci garau-garau har a jefa maka ‘yar tsokar nama. To inda tsiyar ta ke, idan ka je Amurka a can dala 1 babu abin da za ta yi maka.”
A ƙarshe ya bada shawarar cewa a yanzu da farashin ɗanyen mai ya yi sama a kasuwar duniya, ya kamata Kwamitin MPC na Bankin CBN ya samar da ayyukan yi sosai a ƙasar nan.
PREMIUM TIMES Hausa ta bada labarin yadda darajar naira ta faɗi warwas daga naira 504 zuwa naira 522 kowace dala ɗaya, kwana ɗaya bayan sanarwar daina sayar wa ‘yan canji kuɗaɗen ƙasashen waje da CBN ya yi.
Discussion about this post