ZAMFARA: Ƴan bindiga sun kashe Dagacin Lamba, sun sace manoma 20 a gonakin su

0

Manoma akalla 20 ne ƴan bindiga suka sace a a daidai suna gonakin su a karamar hukumar Shinkafi, jihar Zamfara.

Wani mazaunin garin Lamba, dake karamar hukumar Bakura ya shaida wa wakilin mu cewa maharan sun kashe Dagacin ne ranar Juma’a da yamma kuma sun bishi ne har gida suka kashe shi.

Bayan haka a karamar hukumar Shinkafi ƴan bindiga sun sace mutane da dama a kauyuka dabam dabam da suka hada da mutum 20 a kauyen Mabera, sama da mutum 20 a kaiyen Badarawa Kware da Kurya, mutum 1 a kauyen Shanawa, Mutum 3 a Shinkafi, an harbi mace ɗaya da bindiga, sannan sun sace shanu 14, kuma har yanzu ba a ga wasu mutane da dama ba.

Sakataren ƙaramar hukumar Shinkafi Abubakar Atiku ya tabbatar da aukuwar wannan hare-hare.

Jihar Zamfara, na daga cikin jihohin yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya da hare-haren ƴan ta’adda da ƴan bindiga yayi muni matuka.

Kusan kullum sai an yi garkuwa da mutane, kuma an kashe wasu.

Baya ga jihar Zamfara, Jihohin Kaduna da Katsina suma ba a cewa komai.

A jihar Kaduna har yanzu a kwai yaran makaranta masu yawan gaske dake tsare hannun ƴan bindiga.

Gwamnatin jihar ta ce sai dai fa ƴan uwa su tattauna da mahara amma ba ta sahun gwamnatin da ke biyan kudin fansa.

Abu sai kara muni ya ke yi, gwamnati kuma na ci gaba da cika baki cewa ta gano bakin zaren, nan ba da daɗewa ba za a gama da mahara a faɗin yankin.

Share.

game da Author