Allah yayi wa fitacciyar jarumar wasan fina-finan Kannywood, Zainab Booth rasuwa.
Zainab ta rasu ranar Alhamis, kamar yadda jarumi Ali Nuhu ya bayyana a shafinsa ta Instagram.
” Allah yayi wa Hajiya Zainab Rasuwa.Gobe za ayi jana’izan ta gidanta dake kallonPremiere Hospital a court road da Karfe 8 na dsafe. Allah ya ji kanta da rahama, Amin”
Haka kuma jaruman Kannywood sun rika saka hotunan jarumar suna yi mata addu’ar Allah ya khyautata makwanci.
Marigayiya Maryam Booth ce mahaifiya fitacciyar Jarimar Kannywood, Maryam Booth.