Ministan Tsaro Bashir Magashi ya bayyana cewa za a damƙe tare da hukunta dukkan wani mai ɗauke da makami ya na kai wa jami’an tsaro hare-hare.
Magashi ya yi wannan bayani da gargaɗi a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan kammala bikin manna wa Sabon Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Faruk Yahaya lambar zama Laftanar Janar, wadda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi masa.
Ya ce an ɗora wa Sojojin Najeriya haƙƙi bi su na zaƙulo masu ɗauke da muggan makamai a duk inda su ke cikin ƙasar nan.
Gargaɗin Ministan ya zo ne daidai lokacin da ake ci gaba da ƙara samun taɓarɓarewar tsaro a ƙasar nan, sanadiyyar yawaitar muggan makamai a hannun mahara, ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Yawaitar waɗannan hare-hare sun haifar da kisan dubban mutane da garkuwa da dubban mutane, musamman a Arewa.
Idan ba a manta ba, Tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Abdulsalami Abubakar, ya bayyana cewa muggan makaman da ke hannun mahara da ‘yan sunƙuru a ƙasar nan sun kai adadin manyan bindigogi miliyan 6.
Kokarin Daƙile Matsalar Tsaro:
Magashi ya shaida wa manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa cewa an ɗora wa Laftanar Janar Yahaya nauyin tashi tsaye haiƙan ya daƙile matsalar tsaro.
Ya kuma ce tuni Yahaya ya fara aikin sa ka’in da ɓacin.
“Ina jin ai ba Yahaya kaɗai ba, duk ma wani Hafsan Soja ko na ƙasa ko na ruwa ko na sama, babban ƙalubalen da shi ne ya kawo ƙarshen matsalar tsaro.
“Za mu fara bi ana kama masu ɗauke da makami su na kisa, ƙwace da garkuwa da mutane. Najeriya ba za ta bari a ci gaba da ɓarna da tada hankulan jama’a ba.
Da ya ke magana, Yahaya ya jagorancin sa zai yi matuƙar ƙoƙarin ya ga ya magance tsaro a yankunan da matsalar ta fi muni sosai.