Za a maida duk baƙon da ya shigo Najeriya ba tare da shaidar gwajin korona ba – Gargaɗin Gwamnati

0

Shugaban kwamitin shugaban kasa kan tsare-tsare da kula da ayyukan Koronaa Najeriya, PSC, Boss Mustapha ya bayyana cewa gwamnati za ta maida duk matafiyin da ya shigo skasar nan ba tare da shaida yin rigakafin Korona ba.

Ya ce za a kyale matafiya su shigo kasar nan ne kawai idan suka nuna shaidar yin rigakafin Korona ko kuma shaidar anyi musu gwajin amma basu dauke da ita.

Mustapha ya ce wadanda ƴan kasa kuwa idan suka dawo sai an killace su tukunna kafin a barsu su shiga kasa Najeriya.w

“Ma’aikatan lafiya dake aiki a tashar jiragen sama za su yi wa matafiyi gwaji idan sakamakon ya nuna mutum ya na ɗauke da cutar za a killace shi, dole idan ya ki kuma a maida shi.

Amma idan sakamakon ya nuna cewa mutum baya dauke da cutar za a dai killace shi ne kawai na mako daya.

“Za a rike fasfo din matafiyan sai bayan an kammala tantance su kafin a basu.

Mustapha ya ce idan matafiyi ya ki bin wadannan dokoki, za a maida shi kasar da ya fito.

Idan ba a manta ba a wannan mako ne gwamnatin tarayya ta saka kasar Afrika ta Kudu a jerin kasashen da ta hana mutane daga kasar nan zuwa sannan da mutane daga can sauka a Najeriya saboda yaduwar sabuwar samfurin korona dake yi wa mutane kisan fard-daya wato ‘Delta Variants’.

Gwamnati ta kuma ce sai fasinjoji ‘yan Najeriya da suka dawo kasar sun kiyaye dokokin Korona da aka saka kafin a bari su shiga garuruwan kasar nan.

Gwamnati ta yanke wannan hukunci ne saboda fitinar da ta hango na yiwuwar shigowa da cutar kasar nan

Share.

game da Author