Za a farfaɗo da Kamfanin Ƙarafa na Ajaokuta kafin ƙarshen mulkin Buhari -Inji Ministan Ƙarafa

0

Ministan Ƙarafa da Ma’adinai, Olamilekan Adegbite, ya bayyana cewa nan ba da daɗewa ba za a farfaɗo da Kamfanin Sarrafa Ƙarfe na Ajaokuta kafin ƙarshen wa’adin mulkin Buhari.

Ministan ya yi wannan iƙirarin ne a lokacin da ya ke ganawar musamman da tawagar Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a Abuja.

Ya ce tun cikin shekarar 2020 aka so kamfanin Rasha wanda ya gina masana’antar zai turo tawagar masana domin su duba irin kayan gyara da kayan aikin da ake buƙata sai kuma tantance adadin kuɗin da aikin zai ci.

Minista ya ce an cimma yarjejeniyar farfaɗo da masana’antar tun cikin 2019, lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara ƙasar Rasha, a tattaunawar da ya yi da Shugaba Vladimir Putin na ƙasar.

Ita kuma Gwamnatin Rasha ta umarci kamfanin TPE, wanda ya gina wa Najeriya masana’antar Ajaokuta cewa ya je ya tantance aikin gyara da kuma yawan kuɗin da aikin zai ci kafin a kammala shi.

Idan ba a manta ba, Ministan Ƙarafa ya ce tawagar ƙwararru ta mutum 60 za ta zo domin duba halin da kamfanin Ajaokuta ke ciki.

Ya yi ƙarin hasken cewa tun can da farko an gina masana’antar ce domin sarrafa ƙarafa.

A yanzu ya ce idan aka gyara ta, har ƙarafan da ake yi gangar jikin jiragen sama da na motoci za a riƙa sanarwa a masana’antar.

Ya ce ma’aikatar sa ta horas da matasa hanyoyin sarrafa ƙarafa domin bunƙasa ayyukan raya ƙasa.

Share.

game da Author