Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna, Muhammad Jalige ya bayyana cewa rundunar ‘Yan sandan Kaduna ta ceto wasu matafiya a karamar hukumar Jema’a da aka yi garkuwa da su.
Jalige ya ce ‘yan bindigan sun yi garkuwa da matafiya shida a kusa da dajin Bade.
” Bayan ‘yan sanda sun samu labarin harin sai suka bi sahun ‘yan bindigan. An ceto mutum hudu cikin 6 da aka sace.
Bayan haka kuma rundunar ‘yan sanda sun damke wani Musa Danyaro wanda ke kera bindigogi layin Nagogo dake Malali, cikin garin Kaduna. Bayan bindigar da aka samu tare da shi an kuma samu wata babbar bindiga mai baki biyu a gidan sa.