Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina sun fatattaki wasu mahara da suka kai farmaki a layin Minista dake karamar hukumar Malumfashi a jihar.
Kakakin rundunar Gambo Isah ya sanar da haka wa manema labarai a garin Katsina ranar Litini.
“A ranar 17 ga Yuli da misalin karfe 11:02 na dare wasu mahara dauke da manyan bindigogi a bisa babura suka datse hanyar zuwa layin Minista kuma suka yi garkuwa da wani mutumin mai shekara 45 da shi kuma ya fito ne daga kauyen Tafkin Jege, karamar hukumar Kafur.
“DPO din Kankara tare da ‘yan sanda cimma maharan a Unguwar Nakome dake kauyen Yargoje a karamar hukumar Kankara inda a nan suka yi bata kashi tsakin su da maharan.
Bayan haka Isah ya ce ‘yan sanda da misalin karfe 5 na safiyar 17 ga Yuli sun yi arangama da wasu yan bindiga. Sun yi nasarar kwato shanu 36 da suka yi garkuwa da su.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda mahara suka kashe mutum 18 a kauyen Tsauwa dake karamar hukumar Batsari.
Mazauna kauyen sun ce akwai yiwuwar maharan sun kawo harin daukan fansa ne domin a ranar Juma’ar data gabata jami’an tsaro sun fatattaki wasu mahara da suka kawo farmaki kauyen.
A wannan rana jami’an tsaron sun kashe mahara uku daga cikin su.
Mazaunan kauyen sun ce maharan sun cinna wa gidaje da rumbunan hatsi wuta sannan sun saci dabbobi da dama daga kauyen kafin suka koma daji.