‘Yan Sanda sun bankaɗo ‘masana’antar buga jarirai’ a Legas

0

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas sun bayyana cewa sun bankaɗo wani gidan da ake tara matan da ake ɗirka wa ciki su haifi ‘ya’yan a biya su, wato ‘baby factory’.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Legas, Hakeem Odumosu ne ya bayyana haka a ranar Laraba, a Legas.

Ya ce An damƙe wata mata mai shekaru 60 mai suna Augustina, wadda ita ce mai ‘kamfanin buga jariran’.

An kama ta a ranar 1 Ga Yuli, cikin wani gida da ke kan Titin Lawson da ke Isolo, Legas.

“An tsegunta wa jami’an ‘yan sanda abin da ke faruwa a gidan. Sun je sun fito da wasu mata biyu masu tsohon ciki, ɗaya mai shekaru 32 ɗaya kuma mai shekaru 20.

Matar da ke wannan ɗanyen sana’a da matan da aka ceto a cikin gidan duk sun yi wa jami’an tsaro ƙarin haske .

Share.

game da Author