Yan bindiga masu yawa sun afka wani kantin siyar da kayan masarufi inda suka yi fashin kayan abici da suka hada da katan-katan din taliya, shinkafa, sikari da da sauransu.
Bayan kayan abinci da suka sace sun kwashi tsabar kudi har miliyan 1 a wannan kanti mai suna ‘Uzorbest’ dake Onu Asara a jihar Enugu.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa maharan sun shiga wannan kanti ne ranar Litini da misalin karfe 6 na yamma.
Maharan sun sace buhunan shinkafan gida da na waje, masu nauyin kg 10, katan-katan din taliya 30 da buhunan semolina 5.
Sannan sun dauke baban tukunyar iskar gas guda hudu a wani shago dake kusa da kantin.
Wani dake aiki a kantin ya ce ‘yan bindigan sanye da bakaken kaya sun kai mutum 15.
“Da na hango su a cikin mota kirar Toyota Hilux na dauka jami’an tsaro ne amma sai na ga daga shigan su kantin sai suka fara raruman buhunan shinkafa sai ni kuma a rashin sani na hau daya daga cikin su da kokawa.
“Ganin babban bindigan da wani cikin su ke dauke da shi ya sa na cika wa wandona iska na arce.
“Sun loda kayan abincin da suka sata a cikin motoci uku da suka zo da su sannan suka rika yin harbi a sama domin tsorata mutane.
Ma’aikacin ya ce ko kobo ba su karba daga hannun su ba sannan babu wanda ya ji rauni.