Yadda yunwa ke ƙara ruruta wutar matsalar tsaro a yankin Barno, Yobe da Adamawa

0

Hujjoji da dalilai masu tabbatar da barazanar yunwa na ƙara darkakar mutum miliyan 4.4 a yankin, waɗanda a cikin su yanzu haka mutum sama da 775,000 ba su da abincin yau ballantana na gobe, kuma babu siɗi balle saɗaɗa.

Amina Adamu mai shekaru 25 ta saba da yunwa, ta zame mata jiki, domin tare su ke kwana su na tashi babu ranar raba wannan ƙawancen tilas da su ka ƙulla.

Ta kan shafe kwanaki babu abinci. Wasu lokuta kuma ta kan shafe wata ɗaya ta na ɗan cin lomar tuwon nan da ake kira ci-kar-ka-mutu.

A cikin ‘yar bukkar da ta ke kwana a Sansanin Masu Gudun Hijira na Elmiskin da ke Jere kusa da Maiduguri, a Jihar Barno, Amina na ɗaya daga cikin ɗimbin waɗanda ke kwana su na tashi da yunwa sanadiyyar ƙarancin abinci.

Na Shafe Shekaru 5 Ina Dogaro Da Abincin Agaji, Shi Ɗin Ma Yanzu Na Kai Wata Uku Ban Samu Ba -Amina

Amina ta shaida cewa ta shafe shekaru biyar ta na dogaro da abincin agaji. To ƙarin abin da ya firgita mata rayuwa shi ne yanzu haka an kai watanni uku kenan, abincin agajin ma ya faskara.

A yanzu a sansanin, mata masu juna biyu da masu shayar da jira-jirai ne kaɗai ake bai wa abincin agaji da jinƙai.

Mazauna Sansanonin Masu Gudun Hijira irin su Amina da dama sun dogara ne kan ɗan abincin agaji da tallafin da ake bayarwa.

Shi ɗin ma ya na samun cikas saboda yawan kai wa ‘yan ƙungiyoyin agaji hare-hare an kashe wasu, sannan kuma an yi garkuwa da wasun su. Wannan ya na haifar da cikas da tsaiko wajen raba wa mabuƙata abincin tallafi a sansanonin masu gudun hijira.

Yadda Ƙaddarar Zaman Sansanin ‘Yan Gudun Hijira Ta Ritsa Da Ni -Amina:

“Shekaru biyar da su ka gabata Ni da miji na sun tsere daga Bama, garin da ke da babban sansanin sojoji kusa da kan iyakar Najeriya da Kamaru. Mun gudu ne yayin da Boko Haram su ka kai mana wani mummunan hari.”

Irin wannan mummunan hari na kisan-wulaƙanci da ‘yan ta’adda ke yi, ya haddasa sama da mutum miliyan 8.7 sun arce sun bar gidajen su, babu shiri, kuma babu ranar komawa, a jihohin Barno, Yobe da Adamawa.

“Mu na kwance da dare mu na cikin barci, kawai sai mu ka fara jin ƙara da rugugin harbin bindigogi. Daga nan fa duk mu ka tsere mu ka yi tafiyar sa’o’i shida a ƙasa. Daga nan mu ka samu motar da ta kai mu Bama, ta sauke mu a tasha.

“Washegari da safe mu ka fara bara domin su samu kuɗin da za mu biya direban da ya ɗauko mu ɗin.” Inji Amina.

Iyalai da yawa sun dogara da noma domin ciyar da kan su da ‘ya’yan su, kamar yadda su ma su Amina da noman su ka dogara.

Amma hare-haren ta’addancin dhcake yi wa manoma ya haifar da tsoro har manoma sun daina zuwa gona. Zaɓi ya rage wa manomi. Ko dai ya tafi gona a sace ko a tsinto gawar sa, ko kuma ya zauna ya rungumi yunwa, ya tsira da ran sa.

Irin wannan mawuyacin hali da manoma su ka shiga a yankunan da tashe-tashen hankula ya yi ƙamari ne ya haddasa bala’in ƙarancin abinci.

“A yanzu mu na ɗinka huluna ne domin samun ɗan taro da sulai. Abin da mu ke yi kenan domin samun ɗan kuɗin kashewa akwai-ya-babu.” Inji Amina.

Yadda Boko Haram Su Ka Yanke Min Rayuwar Jin Daɗi, Na Dawwama Cikin Ƙuncin Rayuwa -Aisha Idris:

Aisha Idris ita ma kamar Amina, matar aure ce mai ‘ya’ya uku wadda ke zaune tare da mijin ta a garin Baga, gari mai albarkar hada-hadar kasuwancin kifi a kusa da Tafkin Chadi. Sai dai kuma rayuwar jin daɗin da su ke ciki ta yanke, a ranar da Boko Haram su ka kai wa garin hari, cikin 2015.

Tun daga waccan rana har zuwa yau tsawon shekaru shida, A’isha na fama da rayuwar ƙuncin da babu ranar fita a cikin ta.

A ranar da aka kai masu farmakin ta rasa yara huɗu, an kashe su. A haka su ka tsallake su ka gudu, su ka bar ‘yan dabbobin su da harkokin kasuwancin kifin da su ke yi duk su ka tsallake su gudu.

A yanzu A’isha na zaune a ɗaya daga cikin Sansanin Masu Gudun Hijira mafi girma a jihar Barno, inda ta ke rayuwa bisa dogara da abincin tallafin da Ƙungiyar Tallafin Abinci ta Duniya (WFP) ke rabawa. WFP bangare ne na Majalisar Ɗinkin Duniya.

“Ina godiya da irin tallafin da WFP ke ba ni na abinci tun daga lokacin da na samu ciki.

“Domin mu samu abincin da ake ba mu ya riƙa isar mu, idan an ba mu na safe, mu kan ajiye mu haɗa da na rana mu ci. Ko kuma mu ajiye na rana, mu haɗa shi da na dare mu ci, don ya ishe mu.” Inji A’isha.

A’isha wadda a Baga su ke da yalwa da wadatar da har maƙwauta su ke cuyarwa, sai aka wayi gari sun shafe shekaru shida kenan a sansanin da su ma abincin sai an tallafa masu.

Rayuwar Tsaka-mai-wuya: Ka Zauna Cikin Yunwa Ko Ka Saida Rai Ka Tafi Gona Ka Rasa Rai:

Ba ma harsashen bindiga ne kaɗai ke kashe mutane ba ko jefa su cikin ƙunci da muwuyacin hali. Bala’in yunwa kaɗai ya isa kashe mutum a yankin, ko ya nukurkusar da shi, ta yadda ba zai iya amfana wa kan sa komai ba, saboda rashin ƙarfi, sai dai ya dogara da tallafin abinci kaɗai a rayuwar sa.

Babu wanda zai iya faɗa da mai ɗauke da bindiga alhalin ya na fama da yunwar shekaranjiya da ta jiya, har ma da ta yau a cikin sa.

Ta kai ga hatta mutanen da ke zaune a sansanonin amai gudun hijira ana kai masu hari. Idan su ka koma gaeuruwa ko ƙauyukan da su ma abincin ba isar su ya yi ba, duk sai yunwa ta rafke su, babu mai iya tayar da wani. To irin wannan rayuwa ce miliyoyin mutane ke yi a wannan yanki.

Annobar korona ta ƙara ruruta matsalar sosai, musamman wajen tsaikon kasa kai kayan abincin tallafi a yankuna ko kuma matsalar sayen kayan abincin da ya kamata a raba masu.

Sai dai yanzu sosai Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran ƙungiyoyin bayar da tallafi da agaji su na ci gaba da haɗa ƙarfi dare da rana domin tabbatar da cewa al’umma waɗanda ke cikin wannan halin ƙunci su na samun wadataccen abincin da za su ci su rayu.

Share.

game da Author