Yadda ‘Yan bindiga suka kashe Manjo Janar Hassan Ahmed a hanyar Lokoja-Abuja

0

Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana cewa wasu Yan bindiga sun kashe wani babban dakare a rundunar Manjo Janar Hassan Ahmed a hanyar Lokoja zuwa Abuja.

Kamfanin dillancin Labaran Najeriya da ya ruwaito labarin ya rubita cewa Kakakin rundunar sojin Onyeama Nwachukwu ne ya tabbatar da kisan Janar din yana mai cewa Yan bindiga sun bude wa motar Janar din wuta a lokacin da ya ke kokarin dawowa Abuja daga Lokoja.

” Rundunar Sojojin Najeriya na tabbatar da rasuwar Janar Hassan Ahmed wanda Yan bindiga suka kashe a hanyar Lokoja-Abuja ranar Alhamis. Za ayi janaizan sa ranar Juma’a a Abuja.

Ya Kara da cewa tuni babban hafsan Sojojin Najeriya Faruk Yahaya ya aika da tawagar musamman ga iyalan marigayi Janar Hassan Ahmed, domin Yi musu ta’aziyyar rasuwar sa.

Share.

game da Author