Rundunar’yan sandan jihar Adamawa ta kama wani magidanci mai suna Hammawa Usman mai shekaru 41 wanda ya kashe matarsa Rabiatu Usman mai shekaru 36 da tsananin duka kan rancen naira 1,000.
Kakakin rundunar ƴan sandan Suleiman Nguroje wanda ya sanar da haka ranar Alhamis ya ce wannan abin ban haushi da takaici ya auku ne bayan kwanaki bakwai da rundunar ta kama wani magidanci da ya kashe matarsa shima a jihar.
Nguroje ya ce rundunar ta kama Usman a kauyen Ganye dake karamar hukumar Ganye bayan wani dan uwan matar ya kawo kara ofishin su.
Ya ce Usman ya kashe matarsa Rabiatu saboda ta tambaye shi ya biya ta naira 1000 da ya ranta a wurinta.
“Wannan tambayan da Rabiatu ta yi ya bata wa Usman rai daga nan sai ya fusata ya ko haɗa kanta da bango, nan take ta faɗi kasa sume.
“Sai dai ko da aka kaita asibiti nan take likita ya ce tuni ta zama gawa, wato ta rasu.
Nguroje ya ce sakamakon binciken da suka gudanar ya nuna cewa Usman ma’aikacin karamar hukumar Ganye ne kuma sun shekara 16 tare da mijinta, kuma ƴaƴan su biyar.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Aliyu Alhaji ya yabawa ƴan sandan na kama Usman da suka yi don a hukunta shi.
Sannan ya hori mutane da su rika tona asirin mutane irin su Usman wato masu yin ganganci irin haka sannan da cin zarafin matayen su a gidaje.
Discussion about this post