Yadda Shirin N-Power ke zaburar da miliyoyin matasa su taka tudun dogaro da kai, Daga Aliyu Ali Kawaji

0

Shamsuddeen Surajo ya daɗe ya na gaganiyar yadda zai samu hanyar dogaro da kai, maimakon zaman jiran aikin da bai san ranar samu ba.

Faɗi nan tashi can, har Allah ya sa ya yi gamo-da-katarin samun aikin N-Power. Ɗan alawus ɗin da ya riƙa samu bai almubazzarantar da su ba. Sai ya riƙa tara ƙudin sa a banki.

Bayan wa’adin aikin sa ya ƙare, Shamsuddeen ya nemi ƙarin gudummawa wajen abokan sa, inda ya buɗe shagon ɗinki a Hausawa, Kano.

“Wato a baya idan Sallah ta zo ko ɗinki ba na iya yi wa kai na. Amma a yau Ni ne har layi masu kawo ɗinki ke yi a shago na. Ka ga kuwa wannan rufin asirin fa sanadiyyar N-Power ne.

“Shi ya sa a yanzu da aka buɗe ‘Batch C’, na riƙa nuna wai matasa muhimmancin aikin N-Power.” Inji shi.

Irin yadda Shamsuddeen ke yabo da godiya ga shirin N-Power, haka za ka ji duk inda matasa su ke a faɗin ƙasar nan babu wani zance a bakin su mafi ma’ana ko muhimmanci ga inganta rayuwar su, kamar N-Power. A yanzu ko hirar ƙwallon ƙafa ba ta kai N-Power shiga zukatan matasa ba.

Shirin N-Power shiri ne a ɗaya daga cikin tsare-tsaren da Gwamnatin Tarayya ta bijiro da shi, kuma ya ke ƙarƙashin Ma’aikatar Jinƙai, Ayyukan Agaji da Inganta Rayuwar Jama’a.

A yanzu wannan shiri ya na a sahun gaba da gwamnatin tarayya ke tinƙaho da shi a sahun tsare-tsaren fitar da mutum miliyan 100 daga ƙangin talauci, wanda wannan gwamnati ta ƙudiri aniyar tabbatarwa.

Akwai albarka mai dimbin yawa a shirin N-Power. Baya Inganta rayuwar marasa galihu, shirin ya na zaburar da masu cin moriyar sa su koyi dabarun tattalin tara kuɗaɗen kama sana’ar dogaro da kai.

Shirin N-Power rufin asirin iyali ne, domin idan mutum miliyan ɗaya su ka amfana, kowane zai iya ciyar da yara uku. Kenan tamkar an inganta rayuwar mutum miliyan huɗu kenan.

Duk wanda ya amfana da N-Power daga nan ya ke miƙewa hanyar dogaro da kai.

Isma’il Abubakar kuwa cewa ya yi, “Ka gan ni nan, suna na har ɓacewa ya yi saboda ina yawan kiran N-Power. Sai ake ce min “N-Power”. Saboda shirin N-Power ya maida ni mutum. Na amfana kuma na san waɗanda su ka amfana da shirin masu yawan gaske.” Inji shi.

‘Shirin N-Power Na Batch C’: Gabatowar Inganta Rayuwar Matasa Miliyan Ɗaya

A ranar 11 Ga Maris aka buɗe rumbun shiga a cika fam na N-Power ‘Batch C’ a ƙarƙashin Shirin Inganta Rayuwar Jama’a (NASIMS). Tun a ranar da aka buɗe aka sanar da cewa a zabura a cika fam a intanet kuma a shirya yin gwaji na dole kan duk wanda ya shiga ya cika fam ɗin.

Yayin da aka shiga watan Mayu har sama da mutum miliyan 1.8 sun cika fam. Sai dai kuma bayan an tantance, an zaƙulo sunayen mutane 550,000, waɗanda a cikin su ne za a rauraye, a ɗauki mutum 500,000 aikin N-Power a Rukunin Farko na ‘Batch C’.

Daga nan kuma ɗaukar mutum 500,000 zai sake biyo baya, a matsayin cikon mutum miliyan ɗayan da ke ƙarƙashin ‘Batch C’ kenan.

Saboda haka ne Ma’aikatar Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta sanar cewa waɗanda su ka cike fam su riƙa tuntuɓar 08188883416 ko 08176551162 domin neman ƙarin bayani. Ko kuma e-mel: support npower@nasims.gov.ng.

Aliyu ya rubuto daga Abuja.

Share.

game da Author