Yadda mahara suka sake yi garkuwa da shugaban kungiyar kwadago na jihar Taraba a karo na biyu

0

Masu garkuwa da mutane sun sake sace shugaban kungiyar kwadago na jihar Taraba Peter Jediel.

An yi garkuwa da Jediel da misalin karfe uku na daren Lahadi a gidansa dake Sunkani a karamar hukumar Ardo-Kola.

Wannan shine karo na biyu da masu garkuwa da mutane ke sace Jidiel a jihar Taraba.

An fara yin garkuwa da Jediel a watan Fabrairun 2021.

A wancan lokacin wato karon farko Jediel ya yi kwanaki biyu a hannun masu garkuwa da mutanen sannan sun sake shi bayan an biya kudin diyar sa.

Share.

game da Author