Kakakin rundunar Sibul Difens Hamza Illela ya bayyana yadda jami’an rundunar suka damƙe wani ƙasurgumin ɗan bingan Bello Galadima a Sokoto.
Illela ya ce a ranar Talata jami’an rundunar suka yi wa wa Bello diran bazata a Unguwar Hamma Ali a wani shagon saida magani ya na siyan maganin ƙara ƙarfin maza.
Kwamandan rundunar ya yabawa mutanen gundumar Hamman Ali kan bayanan sirri da suka baiwa jami’an tsaron.
Discussion about this post