Yadda hayakin janareto ya kashe mutum hudu cikin dare

0

A kauyen Sanmora dake karamar hukumar Irepodun a jihar Kwara hayakin janareta ya yi ajalin mutum hudu a gida daya.

Makwabta sun bayyana wa manema labarai cewa su dai sun wayi gari ne da wajen karfe bakwai na safiyar Laraba sai suka iske gawarwakin wadannan mutane hudu yan gida daya.

Makwabtan sun bayyana cewa maigidan, matarsa, kawar matarsa, ‘ya’yan su da abokin daya daga cikin ‘ya’yan ne suka zo kauye hutun Sallah daga jihar Legas.

Su wadannan baki sun zo hutun babban Sallar garin ne. Da dare yayi su ka zo kwana sai suka kunnan Janarato domin babu wuta haka dai suka barshi barci ya kama su.

A haka dai ashe hayakin janaretan na komawa cikin dakin su kuma suka yi ta shaka. Cikin su mutum hudu suka yi sallama da duniya a sanadiyyar shakar wannan hayaki, biyu biyu kuma Allah yayi suna da sauran rayuwa a gaba, ba su mutu ba.

Makwabtan sun ce sun kai mutum biyu da suka rayu babban asibitin Offa.

Kakakin rundunar Ajayi Okasanmi bayan ya tabbatar da aukuwar wannan al’amari ya yi kira ga mutane da su rika kula da kunna janareto musamman da dare domin gujewa aukuwar irin haka.

Wannan ba shi bane karon farko da hayakin janareto ke kashe mutane. Da dama masana na yin kira ga mutane da su rika hakura da barin shi kunne musamman idan da dare ne.

Share.

game da Author