Yadda Bam ɗin da aka haɗa cikin goran madara na ‘Viju’ ya kashe ɗan shekara 7 a Kaduna

0

” Kamar yadda muka samu labari ni da mahaifin yaron da ya rasu, wani abu ne mai karan gaske ya fashe a hannun yaran suna wasa a waje a unguwar Badarawa Kaduna, kuma nan take ya farka cikin yaro daya mai suna Abubakar Aminu, daga cikin yaran su uku da ke wasa da goran a waje, kuma ya gutsire hannayen sa biyu.

” Shi kuma ɗaya daga cikin yaran da suke wasa tare ya ji rauni a ciki da kuma hannayen sa ne.

Wannan sune irin kalaman da suka rika fitowa daga bakin iyayen wadanda wannan bam ya fashe a hannun su suna wasa.

A ranar Asabar ne bam da aka haɗa shi cikin goran madara na ‘Viju’ ya fashe a hannun wasu yara yan kasa da shekara 7 a daidai suna wasa da shi basu sani ba a unguwar Badarawa dake Kaduna.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, Muhammed Jalige ya sanar cewa kwararru masu binciken a sashen bamabamai na rundunar sun isa wannan wuri kuma sun gudanar da bincike akai .

” Jami’an mu sun isa wannan wuri kuma sun gudanar da bincike akai. Ina so in tabbatar muku cewa da an gano cewa bam ne aka haɗa cikin goran madara ‘Viju’ sukuma wasu yara su uku suka yi wasa da su ba su sani ba, daga baya sai bam din ya fashe.

Sai dai kuma PREMIUM TIMES HAUSA ta yi tattaki zuwa wannan unguwa domin zantawa da mutanen unguwan da kuma iyayen wasu daga cikin yaran da wannan tsautsayi ya faɗawa.

Malam Hassan Lawal, wanda aminin ɗaya daga cikin mahaifin yaran da abin ya faru da, ya shaida mana cewa tabbas wannan abi ya yi matukar tada musu da hankali.

” Ni dai a matsayina na aminin mahaifin ɗaya daga cikin wanda wannan ibtilai ya afka wa, wato Mal Aminu, mun shiga cikin dimauwa da ruɗani matuka a lokacin da muka ji afkuwar abin.

” Shi mahaifin yaron da ya rasu ya kawo yaran wajen kakanninsu ne dake zaune a unguwar. Ɗaya dan sa ne ɗaya kuma ɗan kanin sa ne.

” Bayan ya tafi ya barsu suna wasan su a gidan, daya daga cikinsu kin wanda bai samu rauni ba ya shaida cewa wani ne ya zo wucewa ya basu wani ruban madara na yara, su kuma suka yi ta kokarin bude ruban su sha madaran sai kawai abin ya fashe.

” Amma kuma da yake yaro ne sai ya ce wun tsinci roban ne a cikin gida suka yi kokarin budewa.

Lawal ya ce sun gaggauta kai yaran da suka ji raunin asibiti, amma cikin ikon Allah, shi yaron Malam Aminu ya cika a daidai ana shiga da shi Asibitin Barai Dikko dake Kaduna.

” An miko mana gawar sa muka yi jana’izar sa da safiyar Lahadi.

Shi kuma dayan ƴaron na can asibiti kwance ana duba shi, domin har an yi mishi aiki a cikin sa da hannayensa.

Rundunar ƴan sanda ta ce ta na ci gaba da bincike akai domin gano waɗanda ke da hannu a aikata wannan abu.

Share.

game da Author