Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa Amurka CDC ta bayyana cewa an gano kwayoyin cutar ƙuraje ‘Monkey pox’ a jikin wani dan Najeriya dake zama a kasar.
Hukumar ta ce wanda ya yo dakon cutar mazaunin Amurka ne amma ya tafi Najeriya ziyarar ƴan uwa da abokan arziki, a can ya ɗauko cutar.
Matafiyin na kwance a asibitin Dallas likitoci na duba shi.
CDC na neman fasinjojin da suka yi tafiya da wannan mutum domin a tabbatar ba su kamu da cutar ba wajen cudanya da aka yi wajen tafiya.
Cutar monkey pox ya fara bullowa ne a shekarar 2003 inda a lokacin mutum 50 suka kamu da cutar.
A Nahiyar afrika kuwa citar ta bayyana ne a shekarar 1970 a Nahiyar Afrika.
A Najeriya cutar ta fara bullowa a shekarar 1978.
Rahotanni sun nuna cewa namun daji kamar su birai da beraye dake gidajen mutane na daga cikin ababen dake kawo cutar ‘Monkey Pox’.
Sannan zazzabi, yawan jin gajiya a jiki, ciwon jiki musamman baya, kumburin jiki musamman idan cutar ta fara nunawa, fitowan kuraje a jikin mai dauke da cutar na daga cikin alamun cutar.