Yadda ƴan sandan Kasar Benin suka damke Sunday Igboho a Kwatano

0

Gogarman dan ta-kifen yankin Yarabawa, Sunday Igboho ya shiga hannu a Kwatano bayan ƴan sandan kasar sun damke shi ranar Sallah.

Ƴan sandan Kwatano sun damke Igboho ne a daidai yana ƙoƙarin arcewa zuwa kasar Jamus in da nan yana da shaidar zama ɗan ƙasa.

Sai dai wani lauyan Igboho ya bayyana cewa Igboho da kan sa ya so a kama shi wato ya mika kan sa ga ƴan sandan Kwatano amma ba wai kama shi a ka yi ba domin ba a isa a kama shi ba sai idan ya so.

Shi dai Sunday Igboho ya sha alwashin sai ya yakice yankin Yarabawa daga Najeriya saboda wai mulkin Buhari ba ta yi wa ƴan yankin adalci.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin barazanar hargitsa zaben 2023 a dukkan jihohin Kudu maso Yamma da gogarman yayi a cikin watan Mayu.

Igboho ya yi wannan cika-baki a Osogbo, babban birnin jihar Osun, wurin gangamin rajin ballewa daga Najeriya.

Ya yi ikirarin cewa gwamnonin jihohin Yarabawa da dama na son ballewa daga Najeriya, amma su na tsoron idan su ka fito fili su ka ayyana bukatar su, za a daina turo masu kudade daga gwamnatin tarayya.

Ya ce gwamnonin na goyon bayan kafa Kasar Yarabawa, amma tsoro ya hana su fitowa su furta.

“Ba mai iya rufe min baki ko yi min wata barazanar tsorata ni. Mu yanzu ba a cikin Najeriya mu ke ba. Babu ruwan mu da Najeriya. Kuma ba za mu sake hadewa da su ba.” Inji Sunday Igboho.

Ba wannan ne barazana ta farko da ya taba yi ba, ko a cikin Yuli yayi kira ga ƴannƙabilar Yarabawa su fito kwann su da kwarkwata su yi zanga-zanga a Legas na neman yakice wa daga Najeriya.

Share.

game da Author