Mazauna unguwar Gimbiya dake Sabon Tasha, garin Kaduna sun tashi da safiyar Alhamis cikin tashin hankali bayan wasu ƴan be na ga sun afka musu cikin daren Laraba.
Mahara sun afka wa wannan unguwa ne cikin dare a na harbi ta ko ina don tsorata mutane sannan suka dunguma zuwa gidajen mutane suna sace su.
” Wannan salo na yin garkuwa da mutane ya bamu tsoron gaske, domin don ka garkame gidan ka da kwaɗo ko ka saka waya a saman katangar duk ba wani abin damuwa ba ne gare su. Katanga suke fasawa ko kuma ma bangon ɗakin ka ta waje sai su rusa shi su shigo maka daki.
” Mutum ya na barci cikin dare sai kawai yaji ana dukan bangon ɗakin sa da guduma ta waje. Da ya ɓurma sai su afko maka cikin ɗaki su yi awon gaba da kai. Haka suka rika yi gashi nan sun tafi da mai gida da ƴan haya.” Haka mazauna wannan unguwa suka rika faɗi wa wakilin PREMIUM TIMES HAUSA.
Ranar Alhamis mazauna wannan unguwa sun tare babban titin da ya ratsa ta Sabon Tasha suna zanga-zangar nuna rashin jin daɗin su kan abubuwan da ke faruwa a wannan Karaman Hukuma.
A cikin wannan mako ƴan bindiga suka sace daliban makarantan sakandaren Bethel wanda har yanzu suna tsare a hannun ƴan bindigan.