Yadda ‘ƴan bindiga suka maida nas-nas din da suka sace a Kaduna masu kula ‘yan uwan su da suka ji rauni

0

Honarabul Yakubu Barde dake wakiltar Chikun/Kajuru a majalisar Tarayy yayi korafin cewa ya samu labarin daga ‘yan uwan wasu ma’aikatan asibiti mata biyu da ‘yan bindiga suka sace cewa sun zama musu masu kula da marasa lafiya sansanin su.

Barde ya kara da cewa yana daga cikin hanya da suka kirkiro yanzu na dauke malaman asibiti suna lunkuyawa da su can cikin daji domin su rika kula da yan uwan su da ak ji wa ciwo.

A tattaunawar da yayi da manema labarai a Abuja, dan majalisan koka kan yadda sace-sacen mutane ya yi tsanani a jihar Kaduna.

Ya ce ‘yan uwan nas-nas din da aka sace sun shaida masa cewa masu garkuwa da mutanen sun ce baza su sake su ba koda sun biya kudin fansar su domin sun zama musu masu kula da marasa lafiya, wato yan uwan su da akaji wa rauni.

” A halin yanzu babu wani abu da za a iya yi da zai sa ‘yan bindigan su saki wadannan mata malaman kiwon lafiya”

” Idan maganan tsaro ne a Najeriya, ina so in tabbatar muku cewa wannan gwamnati ta gaza. Abin ya fi karfinta. Abinda ya kamata gwamnati ta yi shine ta gaggauta neman taimakon manyan kasashe suka zo su gama da wadannan mutanen.

Share.

game da Author