Wahayi aka yi mana daga sama kada mu binne mahaifiyar mu idan ta mutu – Ya’yan wata marigayiya

0

A garin Benin babban birnin jihar Edo wasu mata biyu suka boye gawar mahaifiyar su a cikin gida har na tsawon kwanaki 9 saboda wai an yi musu wahayi kada su binne ta.

Makwabtan wadannan yan mata ne suka gano haka bayan sun binciki gidan ta karfin tsiya saboda wari da ya ishe su a duk unguwar sannan kuma an rasa gane ko menene a gidan yake wari haka.

Wannan abin mamaki ya faru ranar Lahadi.

‘Ya’yan mamaciyar Grace Osagede mai shekara 60 da Theresa Suberu mai shekara 58 sun bayyana wa makwabtan cewa wai Allah ne ya umurce su da kada su binne mahaifiyar su sannan kada su fada wa kowa game da rasuwar ta wahayi da aka yi musu.

‘Ya’yan sun ce bayan sun kiyaye umurnin da Allah ya basu sai suka sanar wa rundunar ‘yan sanda.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kontongs Bello ya ce rundunar ba ta kama Grace da Theresa ba saboda kowa na da ‘yancin yin al’adarsa na gargajiya.

“Sannan abin da Grace da Theresa suka aikata bai saba wa doka ba.

A yanzu dai an kai gawan dakin ajije gawa.

Share.

game da Author